Kishi Ya Sanya Matar Aure Watsa Wa Budurwar Mijinta Ruwan Zafi a Fuska
- Tsananin kishi irin na mata ya sanya wata matar aure ta biye wa son zuciyarta ta aikata aikin dana sani a jihar Bauchi
- Matar auren dai ta haɗa baki da wata ƴar uwarta inda suka lakaɗawa budurwar mijinta dukan tsiya tare da ƙonata da ruwan zafi
- Rundunar ƴan sanda ta yi caraf da matan da suka suka aikata wannan aika-aikar domin gurfanar da su gaban kotu
Jihar Bauchi - Wata matar aure ta faɗa komar ƴan sanda a jihar Bauchi, bayan ta haɗa baki da ƴar uwarta sun ƙona budurwar mijinta da ruwan zafi a fuska.
Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa, a ƙoƙarin aikata wannan aika-aikar, matar auren da ƴar uwarta sun yaudari budurwar mai suna Sa'adatu Liman mai shekara 19 zuwa wani gida da ke a unguwar Gida Dubu a jihar Bauchi, inda suka laƙada mata dukan tsiya.
Ƴan sanda sun tabbatar da aukuwar lamarin
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ya bayyana cewa bayan waɗanda ake zargin sun laƙada mata dukan tsiya, sai suka watsa mata ruwan zafi wanda hakan ya janyo ta samu munanan raunika a wuyanta da kumatunta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan ya fitar a ranar Talata, ya ce waɗanda ake zargin su ne Fatima Muhammad-Sani mai shekara 17 tare da ƴar uwarta Zulaihat Muhammad-Sani, cewar rahoton The Punch.
Ya kuma ƙara da cewa an garzaya da budurwar da aka ƙona zuwa asibiti domin duba lafiyarta.
SP Wakili ya tabbatar da cewa waɗanda ake zargin sun amsa laifin da ake tuhumar su da shi a yayin gudanar da bincike, inda ya ƙara da cewa za a gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abinda suka shuka.
'Yan Daba Sun Sari Dalibin Jami'a a Bauchi
A wani labarin na daban kuma, ƴan daba sun caka wa wani ɗalibin jami'ar Sa'adu Zungur da ke a Gadau cikin jihar Bauchi, wuƙa saboda gardamar ƙwallon ƙafa.
Gardamar ƙwallon ƙafan ta rikiɗe ne ta koma faɗa inda ɗaya daga cikin ƴan daban ya ciro wuƙa ya sari ɗalibin a wuyan hannunsa.
Asali: Legit.ng