Gwarazan Sojin Najeriya Sun Ga Bayan Wasu 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara

Gwarazan Sojin Najeriya Sun Ga Bayan Wasu 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara

  • Sojojin Operation Hadarin Daji sun ragargaji 'yan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara
  • A wata sanarwa da hukumar tsaro ta fitar, ta ce sojojin sun kai samame maɓoyarsu, inda ta sheƙe yan ta'adda uku ranar Litinin
  • Hukumar soji ta roki ɗaukacin al'umma su riƙa taimakawa jami'anta da bayanan sirri kan ayyukan yan ta'adda da sauran masu aikata manyan laifuka

Zamfara - Jami'an sojin rundunar Operation Hadarin Daji sun sheƙe 'yan bindiga uku a jihar Zamfara a wani bangaren kokarin kawo karshen ayyukan ta'addanci a shiyyar Arewa maso Yamma.

Channels tv ta tattaro cewa 'yan bindigan jejin sun gamu da ajalinsu a hannun dakarun sojin Najeriya ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, 2023 a yankin ƙaramar hukumar Bukkuryum.

Sojojin Najeriya a kan hanya.
Gwarazan Sojin Najeriya Sun Ga Bayan Wasu 'Yan Bindiga a Jihar Zamfara Hoto: channelstv
Asali: UGC

Daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaro ta ƙasa, Manjo Janar Musa Danmadami, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a birnin tarayya Abuja ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Rai, Sun Yi Garkuwa da Sarakuna 2 a Jihar Bauchi

Ya ce sojojin sun kai samamen mamaya kan mafakar 'yan bindigan jeji da ke Kairu/Kyaram, karamar hukumar Bukkuyum, inda suka samu nasara bayan musayar wuta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda Sojiji suka yi ajalin yan bindiga 3

A cewarsa yayin artabu da 'yan bindigan, Dakarun soji suka samu nasarar raba uku da duniya kuma suka kwato maƙamai.

A sanarwan, Danmadami ya ce,:

"A yau 12 ga watan Yuni, 2023 (Jiya Litinin), Sojojin Operation Hadarin Daji sun kai samamen kwantan ɓauna mafakar yan fashin jeji da ke Kairu/Kyaram a ƙaramar hukumar Bukkuyum, jihar Zamfara."
"Yayin wannan samame, sojoji sun ci karo da yan ta'adda kuma bayan musayar wuta, uku daga cikin 'yan bindigan suka gamu da ajalinsu."

Hukumar soji ta ja hankalin yan Najeriya

Daraktan ya ƙara da cewa hukumar sojin Najeriya ta yaba wa jami'an rundunar Operation Hadarin Daji bisa wannan nasara da suka samu kan yan ta'adda, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Emefiele Ya Yi Da Suka Bata Wa Tinubu, Gwamnoni, Da Sauran 'Yan Najeriya Rai

Haka nan kuma hukumar Soji ta roki ɗaukacin al'umma su rika taimaka wa Sojoji da bayanan sirri kan motsin yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka a yankunansu.

Yan Bindiga Sun Sace Sarakuna 2 Da Wasu Mutane a Jihar Bauchi

A wani labarin kuma Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai hari kauyuka biyu, sun sace mutane hudu a yankin karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi.

Rahoto ya nuna cewa daga cikin waɗanda maharan suka yi garkuwa da su a harin harda Sarakunan ƙauyukan Balma Anguwan Bakutunbe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262