“Na Tauye Yancin Matata a Matsayin Mai Shari’a”: Sanatan Bauchi Ya Yi Tuntuben Harshe a Bidiyo

“Na Tauye Yancin Matata a Matsayin Mai Shari’a”: Sanatan Bauchi Ya Yi Tuntuben Harshe a Bidiyo

  • Shahararren sanatan arewa ya bayyana muhimmiyar rawar ganin ya taka a rayuwar matarsa wajen yanke hukunci
  • Sanata Adamu Bulkachuwa ya fallasa yadda ya ke sa matarsa, Justis Zainab Adamu Bulkachuwa yi wa takwarorinsa alfarma yayin yanke hukunci a zauren majalisa
  • Ya bayyana cewa Justis Zainab kan take gaskiya a kotunta ga wanda ya fi sakin bakin aljihu, musamman mambobin APC

Adamu Bulkachuwa, sanata mai wakiltan Bauchi ta arewa, ya yi wani gagarumin fallasa game da harkokin matarsa a matsayinta na mai shari'a.

Dan majalisar na Bauchi ya bayyana cewa Zainab Bulkachuwa, matarsa, ta yi amfani da mukaminta a matsayin mai shari'a wajen yi wa takwarorinsa a majalisar dattawa alfarma.

Sanata Adamu Bulkachuwa da matarsa
“Na Tauye Yancin Matata a Matsayin Mai Shari’a”: Sanatan Bauchi Ya Yi Tuntuben Harshe a Bidiyo Hoto:@LawrenceOkoroPG
Asali: Twitter

Sanata Bulkachuwa ya bayyana yadda matarsa ta yi amfani da matsayinta na alkali wajen taimakwa takwarorinsa

Zainab, tsohuwar shugabar kotun daukaka kara ta kasance mace ta farko da ta rike mukamin.

Kara karanta wannan

Wani Matashi Da Ke Gab Da Yin Aure Ya Rasa Ransa Sakamakon Nutsewa A Ruwa A Enugu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana a zauren majalisar dattawa a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, Bulkachuwa ya ce yana yawan rinjayar matarsa wajen yanke hukunci yayin da take kan kujerarta, jaridar The Cable ta rahoto.

"Kuma ta kasance mai hakuri da karbar yadda nake tauyeta sannan ta taimakawa takwarorina," inji shi.

Lawan ya gargadi Sanata Adamu Bulkachuwa

Ahmad Lawan, tsohon shugaban majalisar dattawa wanda ya jagoranci taron ya takewa Sanatan burki kafin ya ci gaba da magana, rahoton, The ICIR.

"Ya mai girma sanata, bana tunanin wannan shawara ce mai kyau daukar wannan hanyar," inji Lawan.

Bidiyon Sanata Adamu Bulkachuwa yana fallasa ya bayyana a intanet

Kalli bidiyon a kasa:

Ana sa ran ganin sunayen ministocin Shugaba Tinubu daga ranar Laraba

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya dauki wasu matakai tun daga rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, kuma hakan ya kara karfin abubuwan da yan Najeriya ke sa ran gani daga gwamnatinsa da yadda ya sanar da cire tallafin mai.

Biyo bayan rantsar da shi cikin abun da ya yi kasa da makonni 2, sabuwar gwamnatin shugaban kasa Tinubu ta yi wasu yunkuri da za a iya daukarsu a matsayin masu tsauri da nuna kishin kasa, kamar sanya hannu a kudirin wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng