Ranar Damokradiyya: Balarabe, Rimi Da Sauran Yan Arewa Da Suka Yi Fafutukar June 12
- Tsohon dan majalisa, Shehu Sani, ya yi martani ga bikin damokradiyya wanda ake yi a ranar 12 ga watan Yuni
- Sani a wata wallafa da ya yi a twitter, ya saki jerin sunayen yan arewa da suka kasance cikin fafutukar June 12
- Da farko shugaban kasa Bola Tinubu ya yi jawabi ga yan kasa a karin farko tun bayan darewarsa kujerar shugabanci a ranar Litinin 29 ga watan Mayu
Tsohon dan majalisar tarayya, Shehu Sani, wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, ya saki jerin sunayen yan arewa da suka yi fafutukar ganin an tabbatar da ranar 12 ga watan Yuni.
Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida, ya soke zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yunin 1993, wanda aka yi ikirarin cewa marigayi MKO Abiola na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ne ya lashe zaben.
A bikin tunawa da June 12 wanda ya zama ranar Damokradiyya a yanzu, Sani ya garzaya shafinsa na Twitter mai suna @Shehusani, inda ya wallafa sunayen yan arewa da suka kasance cikin gwagwarmayar.
Wannan wallafa ta sani na nuna cewa fafatukar 12 ga watan Yuni abu ne na kasa da yan Najeriya daga yankuna daban-daban ma kasar suka bayar da gudunmawarsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shahararrun sunayen da ya ambata sun hada da na tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa, tsohon gwamnan jihar Kano, Abubakar Rimi , tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, Bagauda kaltho.
Sani ya rubuta:
"Yan arewa da suka yi gwagwarmayar June 12: Col Dangiwa Umar, Balarabe Musa,Dr Bala Usman, Alh Ahmed Joda, Sani MFJ, Dr Jibrin Ibrahim, Col Yohanna Madaki, Gambo Sawaba, Salisu Lukman, Suleiman Ahmed, Nasir Abbas, J Danfulani, Ahmed Joda, Lawan Danbazau, Bagauda kaltho, Timothy Bonnet, James Bawa Magaji, Nasiru Kura, Abubakar Rimi (zabe), Sule Lamido (zabe), Arzika Tambuwal, Barister Aliyu Umar, Dan Suleiman, Sanata Bukar Abba Ibrahim, Awesu Kuta, Sanata Abba Moro, Comrade Issa Aremu, Comrade Hauwa Mustapha, Dr Usman Bugaje…”
Shugabancin majalisar dattawa: Dattawan arewa sun bukaci APC ta kyale yan majalisa su yi zabinsu
A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar dattawan arewa ta magantu kan zaben shugabanni a zauren majalisar dokokin tarayya ta 10.
Kungiyar ta bukaci jam'iyyar APC ta baiwa zababbun sanatoci dama su zabi wanda suke so ya ja ragamar harkokinsu ba tare da ta tsoma masu baki ba.
Asali: Legit.ng