Ba Emefiele ba, INEC: Jam’iyyar Peter Obi Ta Nemi a Kwamushe Shugaban INEC, a Yi Bincike a Hukumar

Ba Emefiele ba, INEC: Jam’iyyar Peter Obi Ta Nemi a Kwamushe Shugaban INEC, a Yi Bincike a Hukumar

  • Jam’iyyar Labour ta mayar da martani kan dakatarwar da aka yiwa Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, da kuma kama shi da Hukumar DSS ta yi
  • A martaninta na ranar Asabar, LP ta bayyana bukatar shugaban kasa Bola Tinubu da ya binciki INEC, ba wai babban bankin kasa ba
  • Don haka jam’iyyar adawar ta caccaki matakin da Tinubu ya dauka tare da bayyana cewa ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar

Jam’iyyar Labour Party (LP) ta koka kan dakatarwar da aka yiwa Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

Jam’iyyar Peter Obi ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya binciki hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ba wai bankin kasa ba, inji rahoton Channels TV.

LP ta nemi a bar ta Emefiele, ya binciki INEC
Tsohon gwamnan CBN da ya jawo cece-kuce | Hoto: Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

Jam’iyyar Labour ta mayar da martani kan dakatar da Emefiele, ta bukaci Tinubu ya dumfari INEC

Kara karanta wannan

Abubuwa 4 Da Emefiele Ya Yi Da Suka Bata Wa Tinubu, Gwamnoni, Da Sauran 'Yan Najeriya Rai

A ranar Juma'a, 9 ga watan Yuni, Tinubu ya dakatar da Emefiele saboda binciken da ake yi a ofishin gwamnan na CBN da kuma sauye-sauyen da aka tsara a fannin hada-hadar kudi da tattalin arziki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, kakakin jam’iyyar LP Obiorah Ifo, ya bayyana cewa jam’iyyar ta fusata da hakan, inda ta ye hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, inji rahoton Vanguard.

Bayanan da LP ta yi kan dakatar da Emefiele

A cewar kakakin:

“Abin dariya ne karanta waccar sanarwar saboda yawancin ‘yan Najeriya sun riga sun san manufar gwamnati.
“Idan da gaske, akwai wata hukumar gwamnati da ya kamata a bincika cikin gaggawa, bai kamata a ce hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da shugabanta Farfesa Mahmood Yakubu bane?

Kara karanta wannan

CBN ta zama ATM din munafukan gwamnati: Shehu Sani ya bi ta kan korarren gwamna Emefiele

“Shugabannin jam’iyyar Labour Party sun damu da matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na dakatarwa ko koran gwamnan babban bankin kasa Godwin Emefiele, don ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa kasancewar an yi ba tare da neman izinin majalisar dokokin kasar ba, kuma muna kan matsayar cewa matakin ba daidai bane.”

Naira ta wulakanta a zamanin Emefiele, bincike ya nuna

A wani labarin, rahoton da muka tattara ya bayyana irin wahalar da kudin Naira suka sha a zamanin gwamnan CBN Emefiele.

Rahoton ya bayyana cewa, idan aka yi la’akari da yadda aka faro rike CBN tun 1999, babu inda aka samu matsala kamar na Emefiele.

An kuma ambato yadda kudin kasar ya sha karyewa a zamanin gwamnonin babban bankin a lokuta mabambanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.