“Lokacin da Ya Kamata a Gurfanar Dasu Ya Yi:” Sowore Ya Bayyana Sunayen Abokan Cin Mushen Emefiele
- Wani tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a damke tare da gurfanar da Godwin Emefiele da ‘yan baransa
- Sowore ya ambaci sunayen wadanda yace ya kamata a kama tare da Emefiele kamar haka; Muhammadu Buhari, Abubakar Malami (SAN), da kuma dan uwan Buhari, Tunde Sabiu
- Ku tuna cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Emefiele daga mukaminsa na gwamnan CBN a daren Juma’a sakamakon binciken da ake yi a ofishinsa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC a zabukan 2019 da 2023, Omoyele Sowore, a ranar Asabar, 10 ga watan Yuni, ya ce ya kamata a kama wasu “masu hannu” a kitimurmurar da ka tattare da Godwin Emefiele.
Idan baku manta ba, shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele a matsayin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) a ranar Juma’a 9 ga watan Yuni.
Dakatar da gwamnan na CBN ya biyo bayan binciken da ake yi a ofishinsa da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a fannin hada-hadar kudi, inji gwamnatin Bola Tinubu.
Emefiele: ‘Buhari na cikin wadanda ya kamata a kama’, in ji Sowore
Sowore ya bayyana sunan tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari; da Janar Lucky Irabor, babban hafsan hafsoshin tsaron kasar mai ci a matsayin wadanda ya kamata a kama kan kitimurmurar Emefiele.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa cikin sakon da ya wallafa a Twitter:
“Lokaci ya yi da ya kamata a tuhuma, a kama gurfanar da wadanda ke da hannu a ciki.
“Sun hada da shugabansa, @MBuhari, tsohon Atoni Janar Abubakar @Malami SAN. Dan uwan Buhari kuma tsohon sakataren shugaban kasa, Tunde Sabiu, babban hafsan tsaron kasa, Janar Irabor wanda aka ba matarsa aikin buga kudin Naira a karkashin hukumar Kamfanin Buga Kudi na Najeriya.
"Janar Irabor ya sha tsoma baki a bincike da dama kuma ya hana yin adalci a kokarinsa na kare @GodwinIemefiele daga bincike, kamu da kuma gurfanarwa."
Abin da ya kamata gwamnatin Tinubu ta yiwa Emefiele
A wani labarin, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Reno Omokri ya bayyana kadan daga abin da ya kamata gwamnatin Tinubu ta dauka wajen tabbatar da adalci kan tsohon gwamnan CBN.
A cewarsa, ya kamata gwamnati ta hukunta Emefiele, amma ba a bainar jama’a ba kamar yadda wasu ke ganin ya kamata.
Ana ci gaba da cece-kuce tun bayan da shugaba Tinubu ya bayyana dakatar da gwamnan na CBN da ya dauki tsawon lokaci a kujerar.
Asali: Legit.ng