Binciken Gaskiya: Karya Ne, Babu Hujjar Cewa Dan Shugaban INEC Ya Haukace

Binciken Gaskiya: Karya Ne, Babu Hujjar Cewa Dan Shugaban INEC Ya Haukace

  • Wani ikirari da ba a tabbatar ba ya bayyana a soshiyal midiya kan iyalan Mahmood Yakubu, shugaban INEC, bayan babban zaben Najeriya na 2023
  • Daya daga cikin ikirarin da aka yi a soshiyal midiya ya yi zargin cewa dan Yakubu ya haukace a kasar Saudiyya saboda ta'ammali da miyagun kwayoyi da shan barasa
  • Sai dai, Africa Check ya binciki lamarin sannan ya gano babu wata hujja da ke tabbatar da hakan, kuma cewa kakakin Yakubu ya bayyana lamarin da "labaran karya"

Bayan gudanar da babban zaben 2023 a Najeriya, an yi wani ikirari mara tabbass a kan iyalan Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe na kasa mai zaman kansa (INEC) a soshiyal midiya.

Wani rubutun Facebook da ke yawo a Najeriya a watan Mayun 2023 ya yi zargin cewa dan Yakubu ya haukace a kasar Saudiyya.

Kara karanta wannan

“Sai An Tauna Tsakuwa Idan Za a Kai Najeriya Gaba”: Wike Ya Goyi Bayan Tinubu Kan Cire Tallafin Mai

Shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu
Binciken Gaskiya: Karya Ne, Babu Hujjar Cewa Dan Shugaban INEC Ya Haukace Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images

Rubutun na dauke da shafin labarin da ya alakanta lamarin ga miyagun kwayoyi da shan barasa. Shafin labarin na Facebook ya nakalto wani gidan jarida na kasar Saudiyya a matsayin majiyarsa.

Bugu da kari, labarin ya yi zargin cewa gwamnatin kasar Saudiyya ta bukaci shugaban INEC da ya dauki dansa zuwa Ingila don yin magani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, an yi ikirarin cewa iyalan Yakubu sun gaza nemawa dansu magani a UK da US saboda haramcin da aka sanya masa kan zargin rawar ganin da ya taka wajen kawo karan tsaye ga zaben 2023.

Ikirarin da aka yi dangane da dan Yakubu da kuma zargin rashin lafiyarsa ya bayyana a wasu majiyoyi, ciki harda nan da nan.

Menene gaskiyar ikirarin cewa dan shugaban INEC ya haukace?

Africa Check, wani hukumar binciken kwakkwafi, ya binciki sahihanci ikirarin.

Kara karanta wannan

Tinubu Zai Kara Mafi Karancin Albashi? Shugaban Kasa Ya Yi Sabuwar Sanarwa

A cewar hukumar, kakakin Yakubu, Rotimi Oyekanmi, ya bayyana ikirarin a matsayin "labarin karya" sannan ya bukaci masu karatu da su yi watsi da shi.

A cewar babban sakataren labaran na Yakubu, bayani daga labarin bai da tushe.

"Ikirarin "labarin kanzon kurege ne, dan Allah ku yi watsi da shi", inji Oyekanmi.

Budurwa ta koka bayan ta shiga jirgin sama da wani bodari

A wani labarin kuma, wata matashiyar budurwa wacce ta shiga jirgin sama daga Lagas zuwa Casablanca ta ce akwai wani mutum da ke gurbata iskar da suke shaka.

Matashiyar mai suna @iamrenike a Twitter ta koka cewa fasinjan da take magana a kai yana ta tusa akai-akai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: