“Rayuwa Mai Sauki”: Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Buhari Ke Mike Kafa a Gidansa Na Daura

“Rayuwa Mai Sauki”: Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Buhari Ke Mike Kafa a Gidansa Na Daura

  • Bidiyon tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari yana tafiya a kafa a gidansa na Daura da ke jihar Katsina ya bayyana
  • A cikin bidiyon mai tsawon sakan 15, an gano Buhari a gidansa tare da masu tsaronsa yayin da aka jiyo muryar wata mata tana gaishe shi
  • Yan Najeriya sun yi martani ga bidiyon tsohon shugaban kasar, wasu sun yaba ma saukin rayuwa irin nasa

Daura, Katsina - Yan kwanaki bayan mika mulki ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Eagles Square da ke Abuja, an gano shugaban kasa Muhammadu Buhari a wani bidiyo yana mike kafa a gidansa da ke Daura, jihar Katsina.

Buhari Sallau, daya daga cikin hadiman tsohon shugaban kasar ne ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
“Rayuwa Mai Sauki”: Yan Najeriya Sun Yi Martani Yayin da Buhari Ke Mike Kafa a Gidansa Na Daura Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Ku tuna cewa Buhari da matarsa, Aisha sun koma mahaifarsa Daura bayan rantsar da Tinubu a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu Na Shirin Rage Alawus Din Yan Bautar Kasa? Gaskiya Ta Bayyana

Kalli bidiyon a kasa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yan Najeriya sun yi martani ga bidiyon Buhari yana mike kafa a gidansa na Daura

Wani mai amfani da Facebook, Ahmad Asraj, ya ce:

"Ina farin cikin ganin Jibrin na Sudan, wanda ya koma kasarsa da ke Sudan bayan shugabantar Najeriya na shekaru takwas. Ina taya mutanen Sudan murna kan tarbar dansu, wanda ya shugabanci kasar da irin salo na yan siyasar Najeriya."

Wani dan Najeriya, Abubakar Suleiman, ya ce za a iya koyon abubuwa da dama daga saukin rayuwa irin na tsohon shugaban kasar.

"Akwai abubuwa da dama da za mu iya koya daga rayuwa mai sauki irin Muhammadu Buhari."

Ishaya Maisamari Chullu ya ce:

"Lallai wannan mutumin yana da saukin kai, kawai dai muna yi kamar bama ganinsa ne."

Sai dai kuma, Zeenil Abideen Isa, ya bukaci tsohon hadimina na Buhari da ya dunga wallafa abubuwa kan shugaban kasa mai ci, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Ya Taki Sa'a: Babban Hadimin Tsohon Shugaban Kasa Buhari Ya Samu Aiki Mai Gwaɓi Bayan Karewar Mulki

"Dan Allah yallabai ka yi wallafa kan shugaban kasa mai ci, muna bukatar sanin abun da kasar nan ke ciki."

Umar Sanda Kareto ya rubuta a saukake:

"PMB mun yi kewarka."

Kungiyar kwadago ta yi barazanar shiga yajin aikin gama gari

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar kwadago ta kasa ta yi barazanar shiga yajin aiki saboda cire tallafin man fetur da gwamnatin sabon shugaban kasa Bola Tinubu ta yi.

NLC ta ce idan har gwamnati bata mayar da farashin man yadda take a baya ba toh za su fara yajin aiki daga Laraba, 7 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng