Gwamnan Jihar Sokoto Ya Soke Nadin Dagatai 14 Manyan Sakatarori 23 Da Tambuwal Ya Yi a Jihar
- Sabon gwamnan jihar Sokoto ya soke wasu muhimman naɗe-naɗe da gwamnatin Tambuwal ta yi a jihar kafin ya sauka
- Dr Ahmed Aliyu ya soke naɗin masu riƙe da masarautun gargajiya 14, manyan sakatarori 23 da aka naɗa dab da ƙarshen mulkin Tambuwal
- Ba a bayyana takaimaiman dalilin soke naɗin na su ba, amma majiyoyi sun bayyana cewa an saɓa ƙa'ida wajen naɗin da aka yi musu
Jihar Sokoto - Sabon gwamnan jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu, ya soke naɗin manyan sakatarori 23 da manyan darektoci 15, da gwamnatin da ya gada ta Aminu Waziri Tambuwal, ta yi.
Gwamnan wanda ya fara aiki a ranar Talata, ya kuma dakatar da masu riƙe da sarautun gargajiya 14 da gwamna Tambuwal ya naɗa a jihar, cewar rahoton Daily Trust.
Masu riƙe da sarautun gargajiyar sun haɗa da dagatai 13 da kuma Magajin Garin Sokoto, Alhaji Sama’ila Abdulkadir Mujeli.
Dagatan sun haɗa da Alhaji Aliyu Abubakar III (Ciroman Sokoto) da dagacin Sokoto ta Arewa, Alhaji Buhari Dahiru Tambuwal, Sarkin Tambuwal, Alhaji Ibrahim Dasuki Muhammadu Maccido (Barayan Zaki), dagacin Sokoto ta Kudu, Alhaji Ibrahim Bello Dansarki, Marafan Tangaza, Alhaji Bello Sani Torankawa, Sarkin Yamman Torankawa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ba a bi ƙa'ida ba wajen naɗin da aka yi musu
Ba a bayyana dalilin dakatar da su ba, amma wani mamba a kwamitin miƙa mulki wanda ya nemi a sakaya sunan shi, ya bayyana dalilin dakatar da su yana da nasaba da rawar da suka taka a lokacin zaɓen da ya gabata.
"Naɗin da aka yi musu ya saɓawa abinda al'ummar yankinsu su ke so. Kawai saka musu aka yi saboda goyon bayan da suka nuna ga jam'iyyar PDP a lokacin zaɓen da ya gabata a jihar." A cewarsa
Gwamnan Kano Ya Kori Shugaban Hukumar Alhazai, Sheikh Pakistan, Ɗiyar Sheikh Ja'afar Da Wasu, Ya Naɗa Sabbi
Kakakin gwamnan jihar, Abubakar Bawa, a yayin da yake ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin jihar, ya bayyana cewa za a sake duba kan naɗin da aka yi musu nan bada daɗewa ba domin ɗaukar matakin da ya dace.
Gwamnan Sokoto Ya Sha Alwashin Kwato Ƙadarorin Jihar
A wani labarin na daban kuma, gwamnan jihar Sokoto ya sha alwashin ƙwato kadarorin gwamnatin jihar da aka siyar ba bisa ƙa'ida.
Gwamna Ahmed Aliyu ya ce duk wanda ya san ya amfana da wannan garaɓasar ya gaggauta dawo da ita, ko kuma ta yi aiki a kansa.
Asali: Legit.ng