Sabon Mulki: Kananan ’Yan Kasuwa Sun More, Abba Gida-Gida Ya Yafe Musu Biyan Haraji
- Gwamnatin jihar Kano ta ce ta dauke wa masu kananan sana’o’i biyan haraji da za a fara a watan Yuni mai kamawa duba da yadda rayuwa ta yi tsada
- Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da haka yayin da yace duk masu samun kasa da N30,000 ba za su biya wannan haraji ba a jihar
- Gwamnatin jihar ta ce za ta dawo da bankunan ba da rance ga kananan masana’antu guda 37 don bunkasa tattalin arziki da Kwankwaso ya kirkira
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa masu kananan sana’o’i ba za su na biyan haraji ba da za a fara a watan Yuni mai kamawa.
Gwamnan ya bayyana cewa masu kananan sana’o’i wadanda ba za su biya harajin ba sune wanda kudin shigan da suke samu ya gaza N30,000.
Ya kara da cewa karban haraji a wurin irin wadannan mutane rashin adalci ne saboda yanayin yadda rayuwa ta yi tsada.
Shin wani tsari gwamnatin za ta bi don gane wadanda ba za su biya harajin ba?
Daily Trust ta tattaro cewa gwamnan bai fadi wani tsari ta yadda gwamnatin za ta gane masu kananan sana’o’i da ake magana akansu ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Abba Kabir ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta samar da kyakkyawan yanayi da kuma samar da jari don kananan masana’antu a jihar don bunkasa tattalin arziki.
A cewarsa:
“Zamu dawo da bankunan ba da rance guda 37 da gwamnatin Kwankwaso ta kirkira don habaka harkan kasuwanci, wadannan bankuna su ne gwamnatin Ganduje ta bar su kara zube don samun damar siyar da su ga abokansu da ‘yan uwansu.”
Zababben Gwamnan Kano, Abba Kabir Ya Bayyana Kadarorinsa Ana Dab da Rantsar Da Shi
A wani labarin, zababben gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya bayyana kadarorinsa gabanin rantsar da shi a matsayin sabon gwamna.
Gwamnan ya bayyana kadarorin nasa ne a hukumar da'ar ma'aikata reshen jihar Kano, yayin da ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Asali: Legit.ng