El-Rufai Ya Haramta Wata Kungiyar Kudancin Kaduna Sa’o’i Kadan Kafin Karewar Wa’adinsa
- Gwamnan jihar Kaduna ya alanta kungiyar Atyap a matsayin haramtacciya biyo bayan wasu dalilai na tsaro da ya duba
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ya saura sa'o'i kadan gwamnan ya sauka daga mulki tare da mikawa Uba Sani
- A ranar 29 ga watan Mayu ne Najeriya za ta yi sabon shugaban kasa, haka nan jihar ta Kaduna da ke Arewa maso Yamma
Jihar Kaduna - Kasa da sa'o'i 24 kafin karewar wa'adinsa Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ayyana haramta kungiyar ci gaban al'ummar Atyap a jihar ta Kaduna, Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Muyiwa Adekeye, mai baiwa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa ya fitar ranar Lahadi 28 ga watan Mayu.
Adekeye, ya bayyana cewa, kungiyar ta Atyap ta zama wata kafar da ke da alaka birkita zaman lafiya a jihar da kuma kawo tsaiko kyakkyawan shugabanci na jihar Kaduna.
Ya bayyana cewa gwamnan ya sanya hannu a kan dokar haramtawar ne daidai da sashi na 60 na kundin laifuffuka na jihar Kaduna mai lamba 5 na shekarar 2017, da sashe na 5 (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Zan ci gaba da aiki na har cikar wa'adi na
A karshen makon da ya gabata ne dai gwamnan ya sha alwashin ci gaba da daukar tsauraran matakai har zuwa karfe 11 na daren da gwamnatinsa za ta kare.
El-Rufai zai mikawa Sanata Uba Sani, ranar Litini 28 ga watan Mayu kamar yadda dokar Najeriya ta tanada, Tori News ta tattaro.
Gwamnan ya shafe shekaru takwas yana mulkar jihar Kaduna, kuma an sha fama da rikicin 'yan bindiga da masu satar mutane a yankuna daban-daban na jihar.
Gwamna Ganduje ya alanta masu kwacen waya a matsayin 'yan fashi da makami
A wnai labarin, kunji yadda gwamnatin jihar Kano ta bayyana daukar mataki kan masu kwacen waya da suka addabi jama'a.
A cewar dokar jihar, yanzu duk wani mai satar waya daidai yake da mai yin fashi da makami, kuma za a hukunta duk wanda aka kama.
Ana yawan samun lokutan da 'yan fashi da makami ke kwace waya tare da jikkatawa ko hallaka mutane a Kano.
Asali: Legit.ng