Boko Haram: “Har Yanzu Ina Bakin Cikin Yaranmu Da Ke Tsare” – Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jawabin ban kwana ga daukacin al'ummar Najeriya yayin da yake shirin mika mulki a gobe Litinin
- Buhari ya bayyana cewa har yanzu yana jin kunar zuciya idan ya tuna akwai sauran yaran kasar tsare a hannun yan ta'addan Boko Haram
- Shugaban kasar mai barin gado ya ce har yanzu hukumomin tsaro na aiki don ganin sun kubutar da yaran ba tare da wata tangarda ba
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana jin radadin cewa har yanzu wasu daga cikin yaran kasar na makale a sansanin yan ta'adda.
A wani dan takaitaccen jawabin ban kwana da ya yi a ranar Lahadi, 28 ga watan Mayu, shugaban kasar, wanda zai mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu, ya ce har yanzu ana yaki don ceto yaran wadanda yawancinsu mata ne.
Yanzu Yanzu: “Ba Zan Taba Kiran Tinubu Da Shugaban Kasata Ba”, Shahararren Malamin Addini Ya Magantu
Ya kuma jaddada cewar shirinsu shine ceto yaran ba tare da wata matsala ba, Channels TV ta rahoto.
Premium Times ta nakalto Buhari yana cewa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Har yanzu, ina bakin ciki kan kasancewar yaranmu a tsare, ina taya iyaye, abokai da yan uwan dukkanin wadanda suka rasa masoyansu a zamanin kisan rashin tausayi alhini.
"Ga duk wadanda ke tsare ba bisa ka'ida ba, hukumomin tsaronmu na aiki ba dare ba rana don ceto su ba tare da wata matsala ba."
Gwamnatina ta yi yaki don kare rayukan yan Najeriya, Buhari
Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta yi fafutuka don tabbatar da kare rayukan daukacin yan Najeriya da kare muhallinsu wanda aka cimma nasara.
Ya kara da cewar:
"Yayin da nake kammala wa'adin mulkina, mun yi nasarar rage ayyukan yan fashi, ta'addanci, fashi da makami da sauran laifuka."
A kokarin ganin nasarar da bangaren tsaro suka samu zuwa yanzu, shugaban kasar ya yi kira ga al'ummar Najeriya da su kara zama masu sanya idanu da kuma taimakawa hukumomin tsaro.
Ba zan kira Tinubu shugaban kasata ba, Fasto Bakare
A wani labari na daban, Fasto Tunde Bakare ya bayyana cewa ba zai taba kiran Bola Tinubu da shugaban kasarsa ba.
Shahararren faston Najeriya ya yi zargin cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa na 2023.
Asali: Legit.ng