Gwamnatin Kano Ta Gano Mafita Game Da ’Yan Kwacen Waya, Za Ta Yi Musu Hukuncin ’Yan Fashi da Makami

Gwamnatin Kano Ta Gano Mafita Game Da ’Yan Kwacen Waya, Za Ta Yi Musu Hukuncin ’Yan Fashi da Makami

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana mafita ga yadda za a magance matsalar yawaitar faruwar kwacen waya a Kano
  • A yanzu haka, an alanta ‘yan kwacen waya a matsayin masu aikata fashi da makami, kuma hukuncinsu yanzu daya
  • ‘Yan Kano suna ci gaba da fuskantar matsala bayan da ake yawan samun ‘yan kwacen wata a jihar da ke Arewa maso Yamma

Jihar Kano - Yayin da lamura ke kara tabarbarewa, ake ci gaba da yiwa mutane fashin wayoyin hannu a jihar Kano, gwamnati ta bayyana matsayarta kan fashin.

A cewar gwamnati, daga yanzu ya zama doka cewa, kwacen waya na daidai da fashi da makami, kuma za a huunta duk wanda aka kama, rahoton Aminiya.

Wannan na nufin cewa, duk lokacin da aka kama dan kwacen waya, za a yi masa hukunci ne daidai da wanda kotu ke yiwa ‘yan fashi da makami.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Jerin Manyan Matsaloli 5 da Ke Jiran Tinubu da Zarar Ya Karbi Buhari

An samu mafita ga yadda za a magance matsalar 'yan kwacen waya
Jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya | Hoto: The Nation
Asali: UGC

Wannan batu na fitowa ne daga bakin kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba da sanyin safiyar ranar Asabar 27 ga watan Mayu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin da yasa aka dauki matakin

A cewar kwamishinan, an dauki matakin alanta kwacen waya a matsayin ta’addancin fashi da makami ne biyo bayan taron majalisar zartaswa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta, Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta fahimci cewa, yawaitar kwacen waya da jikkata mutane a jihar babban abin damuwa ne da bai kamata a bari ya ci gaba da faruwa ba.

Hakazalika, ya ce tabbas za a dauki tsauraran matakai na ganin an dakile ci gaba da aukuwar lamarin a yankuna daban-daban na jihar.

Idan baku manta ba, mazauna jihar Kano sun shiga matsanancin damuwa game da yadda ake yawan tare mutane da wukake ana kwace musu wayoyi.

Kara karanta wannan

Shekaru 8 Na Shafe Ina Ceto Yara ’Yan Najeriya Daga Hannun ’Yan Bindiga, Inji Buhari

Yadda Masu Kwacen Waya Suka Kashe Mutane da Yawa a Cikin Birnin Kano

A wani labarin, akalla mutum 6 ne suka rasa rayuwarsu yayin da wasu miyagun 'yan daba masu kwacen waya suka farmaki mutanen Unguwar Kabara da Gwangwazo a Kano.

Daily Trust ta tattato cewa lamarin ya faru da sanyin safiyar ranar Jumu'a kuma ya daga hankulan mazauna Unguwamnin.

An ce masu kwacen sun rika caka wa duk wanda suka gani wuka ba tare da la'akari da shekaru ko jinsi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.