Gwamnatin Buhari Ta Ayyana Hutun Kwana 1 Saboda Bikin Rantsar da Tinubu
- Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 29 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu domin murnar bikin rantsar da sabon shugaban kasa
- Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa ranar Jumu'a
- Ya yi kira ga 'yan Najeriya su haɗa kansu wuri guda su goyi bayan gwamnati mai jiran gado domin ta haka ne kaɗai zata samu nasara
Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta ayyana ranar Litinin 29 ga watan Mayu, 2023 a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan Najeriya.
Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jummu'a a madadin gwamnatin tarayya.
The Nation ta rahoto cewa FG ta ɗauki wannan matakin ne domin baiwa yan Najeriya damar murnar rantsar da zababben shugaban ƙasa na 16 a tarihin ƙasar nan.
Ministan ya taya 'yan Najeriya murnar wannan rana mai ɗumbin tarihi, kana ya yaba musu bisa yarda da tsarin Demokuraɗiyya a zaben da ya samar da zababben shugaban ƙasa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A sanarwan da babban Sakataren ma'aikatar cikin gida, Dakta Shuaib Belgore, ya fitar, Ministan ya roƙi 'yan Najeriya su ci gaba da goyon bayan kokarin bunƙasa Demokuraɗiyya ta hanyar bin doka da oda.
Leadership ta rahoto Rauf Aregbesola na cewa:
"A ko ina demokuradiyya ba ta ƙarewa kuma hanya ɗaya da zata ƙara bunƙasa a samu ci gaba da walwala ga jama'a shi ne bin doka da oda, goyon bayan tsare-tsarenta da kuma bai wa mutane yancinsu."
Ministan ya kuma ƙara da yin kira ga ɗaukacin 'yan Najeriya su ci gaba da zama lafiya tsakanin juna da kuma nuna soyayya ga maƙota, inda ya ce babu abinda zai tafi daidai sai an samu zaman lafiya.
Mista Aregbesola ya buƙaci al'umma su haɗa kai wuri ɗaya su mara wa sabuwar gwamnati mai jiran gado baya domin haɗin kan mutane shi ne tushen ƙarfin Najeriya.
Daga Karshe, Jirgin Saman Najeriya Ya Sauka a Birnin Tarayya Abuja
A wani labarin kuma Bayan dogon lokaci, Jirgin saman Nageria Air ya sauka a filin Nnamdi Azikwe da ke Abuja ranar Jumu'a.
Jirgin saman wanda ya taso daga Addis Ababa, ƙasar Ethiopia, a ɗazun muka kawo muku yadda ya gama shirin lulawa sararin samaniya zuwa gida Najeriya.
Asali: Legit.ng