Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano Ta Wanke Doguwa Daga Zargin Kisan Kai
- Gwamnatin jihar Kano ta wanke Alhassan Ado Doguwa daga tuhume-tuhumen da ake masa ciki harda na kisan kai
- Kwamishinan shari'a na jihar Kano, Lawan Musa Abdullahi ya ce binciken da suka gudanar ya nuna ba a sami Doguwa da laifi ba
- Ana dai tuhumar shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan da harbin wasu a lokacin zabe tare da kona ofishin NNPP
Kano - Ma'aikatar shari'a ta jihar Kano ta wanke shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Ado Doguwa daga tuhumar da ake masa na kisan kai da ta'addanci.
Atoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar, Musa Abdullahi Lawan, ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Kano a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, Daily Trust ta rahoto.
Ya ce:
"Bisa bayanan da aka samu a baya da abubuwan da aka lura da su, ba za mu iya tabbatar da tuhume-tuhumen da ake yi wa Doguwa da suka hada da tayar da zaune tsaye ta hanyar sanya wuta da kisan kai ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mun gaza samun kwakkwaran hujja don alakanta shi da laifukan da ake magana a kai duba ga cewar an samu sabani da dama cikin bayanan da aka samu daga wurin shaidu.
"Jawaban wadanda suka shafawa Doguwa kashin kaza ya yi karo da juna kuma mun gaza samun kwakkwaran shaidan likita don tabbatar da mutuwar mutanen.
"Shari'ar a bayyane take cewa ba za a iya tabbatar da zarge-zargen cewa Doguwa ya kashe mutane ba."
A cewarsa, za a tuhumi takwas daga cikin mutane 12 da aka kama da laifin aikata barna ta hanyar sanya wuta karkashin sashi 336 na dokar Penal Code kamar yadda aka gyara ta.
An samu sabani a bayanan da aka samu daga wurin shaidu
Har ila yau, sashin Hausa na BBC ta rahoto cewa kwamishinan ya ce a yayin da suke gudanar da bincike sun gano cewa ma'aikatan asibiti ba su yi cikakken bincike kan mutanen da ake zargin an harba da bindiga ba, soboda haka ba a iya tabbatar da cewa an harbe su ba.
Ya kuma ce an gudanar da bincike kan bindigogi da harsashai da ke hannun yan sandan da ke tare da dan majalisar a lokacin da rikicin ya faru.
Lawan ya kuma yi bayanin cewa babu wata shaida da ta nuna cewa an yi amfani da bindigogin, kasancewar jami'an tsaron sun mayar da daidai adadin harsasan da ke a hannunsu.
Zargin kisa: Kotu ta ba da umurnin tilastawa Atoni Janar na Kano gurfanar da Doguwa
A baya mun ji cewa a ranar Alhamis, 27 ga watan Afrilu, wata babbar kotu da ke zama a jihar Kano, ta amince da wani kudiri da ke neman a fara tuhumar shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Doguwa kan kisan kai.
Umurnin da kotun ta bayar zai tilastawa Atoni Janar na jihar Kano fara gurfanar da Doguwa a gaban alkali.
Asali: Legit.ng