Kwacen Waya: Fusatattun Matasa Sun Sake Kone Adaidaita Sahu Ta Barayin Waya a Kano
- Wasu matasa a jihar Kano sun kone adaidaita sahu da suke zargin ta masu kwacen waya ne a Kofar Kabuga
- Lamarin ya faru ne a ranar Laraba 24 ga watan Mayu bayan mutane sun fahimci yaran masu kwacen waya ne
- Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya gargadi mutane akan daukar doka a hannu, ya nemi goyon bayansu
Jihar Kano – Wasu fusatattun mutane sun kone adaidaita sahu wanda ake zargin ta masu kwacen waya ne a Kofar Kabuga a karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano.
Lamarin ya faru ne a ranar Laraba 24 ga watan Mayu bayan mutanen su fahimci cewa yaran sun zo ne don kwace wayoyin mutane.
Wani shaidan gani da ido ya tabbatar cewa matasan da suke kwacen wayoyin sun fara ne tun daga Kofar Sarki har zuwa asibitin Nasarawa a karamar hukumar Nasarawa da ke jihar.
“Yan Matan Nan Sun Cancanci Taimako”: Kyawawan Yan Mata Da Ke Aiki a Kamfanin Yin Biskit Sun Burge Jama’a
Bayan mutane sun tinkare su don daukan mataki sai matasan suka gudu kuma suka bar adaidaita sahun a wurin yayin da mutane kuma suka kona ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa:
“Suna yawan zuwa kusan kullum su kwace wa mutane wayoyinsu, shiyasa mutane suka fusata don daukar doka a hannunsu, bayan sun ga gungun jama’a sun nufe su sai suka gudu yayin da mutanen suka kona adaidaita sahun.
“Mutane sun gaji da wannan lamari, yawanci idan an kamasu kafin wani lokaci an sake su, na taba ganin inda masu kwacen wayan suka gudu aka kona adaidaita sahunsu, kafin a kona ta an samu wayoyi fiye da 30 a ciki, abin bakin ciki ma shi ne yadda suke siyarda wayoyin da araha don su sayi kayan maye.
Majiyar ta kara da cewa:
“Suna shiga adaidaita sahu a matsayin fasinjoji don kwacen waya ko su yi amfani da tasu su dauki mutane su kwace musu wayoyi akan hanya.
Kwacen waya ya zama ruwan dare tun bayan zabubbuka
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa kwacen waya ya zama ruwan dare kuma kullum kara tsamari yake tun bayan babban zaben da aka gudanar a farkon shekarar nan, inda aka kwacewa mutane da dama wayoyinsu, aka ji wa wasu raunuka har ma da kashe wasu mutane a kokarin kwacen wayar.
Kwamishinan 'yan sandar jihar ya gargadi mutane
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Usaini Gumel ya gargadi mutane akan daukar doka a hannunsu inda ya bukaci su hada kai da jami’an tsaro don kawo karshen wannan matsalar.
Yan Sanda Sun Kwamushe Barayin Waya Bayan Sun Fasa Shago a Jihar Katsina
A wani labarin, 'yan sandan jihar Katsina sun kwamushe wasu matasa da suka fasa shogo suka saci wayoyi 48.
Kakakin rundunar, CSP Gambo Isah ne ya tabbatar da haka a ranar Juma'a 19 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng