An Daure Lakcara Shekaru 5 a Gidan Kaso Bisa Zargin Sama da Fadi da N6m Na Tallafin Karatunsa
- An tasa keyar wani tsohon lakcara a Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke jihar Kebbi bisa zargin sama da fadi
- Mohammed Nuhu ya mallakar wa kansa wadannan makudan kudade da makarantar ta ware don biya masa tallafin karatu
- Ana zarginsa da sama da fadi da N2m a shekarar 2015 da kuma fiye da N4m a shekarar 2016 wanda aka ware don karatunsa
Jihar Kebbi - An yanke wa wani tsohon lakcara Muhammed Sani Nuhu shekaru biyar a gidan gyaran hali saboda sama da fadi da N6m na Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke jihar Kebbi.
Wanda ake zargin, ya mallakar wa kansa wadannan makudan kudade da makarantar ta ware don biya masa tallafin karatu amma bai yi karatun ba.
Hukumar Dakile Cin Hanci da Sauran Laifuka (ICPC) ce ta kama shi da laifin, yayin da kakakin hukumar, Azuka Ogugua a ranar Talata 23 ga watan Mayu ya ce an gurfanar da shi a babbar kotun jihar da ke birnin Kebbi bisa zargin laifuka guda hudu.
Biyu Babu: Kotu Ta Datse Igiyar Auren Malamin Addini Saboda Yawan Jibgar Matarsa, An Mallaka Wa Matar Dukkan Kadarorinsa
Ana zargin Nuhu da sama da fadi da N2m a shekarar 2015, sannan fiye da N4m a shekarar 2016 wanda aka ware don tallafa masa ya karo karatunsa, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aikata hakan laifi ne wanda ya sabawa dokokin kasa da kuma dokokin hukumar ICPC wanda akwai hukunci mai tsanani ga duk wanda ya aikata wadannan laifuka.
Ya yi sama da fadi da kudin tallafin karatunsa
Rahotanni sun tabbatar cewa Nuhu wanda an kore shi a matsayin lakcara a makarantar, ya karbi kudade don karo karatu da halartar wasu tarurruka masu muhimmanci a Aberdeen na kasar Ingila sannan da digiri na uku a jami’ar fasaha da ke kasar Malaysia.
Daga cikin zargin da ake masa wanda jami’in hukumar ICPC, Mashkur Salisu ya bayyana ya ce Nuhu ya karbi wadannan kudade amma kuma ya yi amfani da su a karan kansa ba tare da zuwa karatun ba.
Hukuncin mai shari'a a kotun
Mai shari’a Hassan Usman ya ba da umarnin daure Nuhu shekaru biyar a gidan gyaran hali kan dukkan zargin da ake masa.
Ya kuma umarci wanda ake zargin da ya dawo da N6.5m wanda shi ne dalilin laifin na shi ga gwamnatin tarayya.
Kotu Ta Datse Igiyar Auren Fasto Kan Jibgar Matarsa, An Mallaka Wa Matar Dukkan Kadarorinsa
A wani labarin, kotu da datse auren wani Fasto bisa zargin yawan jibgar matarsa a jihar Edo.
Fasto wanda ma'aikacin jinya ne ya saba sakin mata da kuma son auren jari da yake yi don cimma burinsa.
Asali: Legit.ng