'Yan Najeriya Fiye Da Miliyan 14 Masu Shekaru 15 Zuwa 64 Ne Ke Ta’ammali Da Kwayoyi, Shugaban NDLEA, Marwa
- Shugaban hukumar NDLEA, Mohammed Buba Marwa ya koka kan yadda ‘yan Najeriya ke amfani da kwayoyi
- Marwa ya bayyana haka ne yayin taron karshen shekara na wayar da kan jama’a wadda hukumar NICO ta shirya
- Ya ce shan kwayoyi yafi yawa a tsakanin matasa wadda ke haddasa matsaloli da suka hada da sace-sace
Abuja - Shugaban Hukumar Hana Sha Da Fataucin Kwayoyi (NDLEA), Mohammed Buba Marwa ya koka kan yadda ‘yan Najeriya ke ta’ammali da kwayoyi musamman tsakanin shekaru 15 zuwa 64.
Buba Marwa ya bayyana haka ne a taron karshen shekara na wayar da kan jama’a wadda Hukumar Wayar da kan Al’umma akan Al’adu (NICO) ta shirya mai taken shan kwaya da kuma makomar matasan Najeriya.
Ya ce shan kwayoyi a tsakanin matasa shi yake haddasa fitintinu da ake fama da su yanzu da suka hada da garkuwa da mutane da karuwanci da fashi da kuma hare-haren ‘yan bindiga, cewar Tribune.
Buba Marwa ya yi godiya ga wadanda suka shirya taron
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Da farko zan fara da godewa wadanda suka shiya wannan taro mai muhimmanci, wannan ya nuna irin jajircewarku don ganin an dakile shan kwayoyi da kuma abubuwan da suke biye da su a al’ummomin mu.
“Wannan taro ya zo a lokacin da ya dace saboda zai kara wayar da kan mutane akan illolin shan kwaya da kuma wayar da kan al’umma akan gudumawar da za su bayar don ganin an dakile wannan lamari da kuma hanyoyin kariya."
Ya bayyana adadin mutanen da ke shan kwayoyi
Shugaban hukumar, kamar yadda Punch ta tattaro a kara da cewa:
”A wani bincike da aka gudanar a shekarar 2018, ya bayyana cewa kusan 14.3m na ‘yan Najeriya masu shekaru tsakanin 15-64 suna amfani da kwayoyin gusar da hankali wadanda ba taba ko giya ba.
“Wadanda aka fi amfani da su sun hada da hodar iblis da wiwi da sauran kwayoyi da ake siya a shagunan magani, abin takaici shi ne duk cikin mutane hudu masu ta’ammali da kwaya, daya daga ciki mace ce, yayin da mutum daya cikin biyar da suke amfani da kwaya ke fama da matsaloli, haka kuma yawan amfani da kwaya ba shi da yawa a tsakanin mutane masu shekaru tsakanin 25 zuwa 39.
NDLEA Ta Ba Da Sako Ga Masu Neman Aikin da Hukumar Za Ta Dauka
A wani labarin, Hukumar NDLEA ta bude yanar gizo domin masu neman aikin hukumar, amma sai aka samu cikas.
Hukumar ta tabbatar musu cewa ana kokarin shawo kan matsalolin da suka faru a lokacin cike-ciken da masu neman aikin ke yi.
Asali: Legit.ng