"Ba Mu Bane" EFCC Ta Ankarar da Yan Najeriya Kan Sabon Salon Damfara da Ya Bullo

"Ba Mu Bane" EFCC Ta Ankarar da Yan Najeriya Kan Sabon Salon Damfara da Ya Bullo

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rasahawa (EFCC) ta ja hankalin 'yan Najeriya su guji wani saƙon damfara mai ɗauke da sunan EFCC
  • Mai magana da yawun EFCC na kasa, Wilson Uwujaren, ya ce sakon ba daga hukumar ya fito ba, wasu ne ke amfani da sunan domin cutar jama'a
  • Ya gargaɗi mutane kan sabuwar hanyar damfarar, inda ya ce duk wanda ya faɗa tarkon kar ya ɗora wa EFCC laifi

Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gargaɗi 'yan Najeriya su guji faɗawa tarkon wani, "Saƙon damfara," da aka kirkiro da sunan taimako daga EFCC.

Hukumar ta bayyana cewa babu wani sashi mai suna, "EFCC Help Desk," kwata-kwata a cikin hukumar, kamar yadda wata sanarwa ta tabbatar.

EFCC.
"Ba Mu Bane" EFCC Ta Ankarar da Yan Najeriya Kan Sabon Salon Damfara da Ya Bullo Hoto: @officialEFCC
Asali: UGC

Wannan gargaɗi na kunshe ne a wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na Tuwita mai ɗauke da sa hannun shugaban sashin midiya da yaɗa labarai, Wilson Uwujaren.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: NAHCON Ta Yi Amai Ta Lashe Kan Ƙarin Ƙuɗin Kujerar Hajjin Bana 2023

Wani sashin sanarwan mai taken, "Scam Alert," ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"An jawo hankalin hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'adi (EFCC) kan wani sakon damfara da ke yawo a Soshiyal midiya da sunan ya fito ne daga EFCC Help Desk mai hedkwata a Jabi, Abuja."
"Domin share tantama da fayyace gaskiya, EFCC ba ta da wannan sashin kwata-kwata, kuma duk wani saƙo da aka kirkiro da sunan EFCC HELP DESK ba daga hukumar EFCC ya fito ba."
"Gurɓatattun da suka kirkiro wannan hanyar damfarar suna amfani da sunan EFCC ne domin lulluɓe zunubinsu, don haka ya kamata mutane su kula domin kar a zargi EFCC idan wani ya faɗa tarkon 'yan damfaran."

Haka nan kuma EFCC ta shawarci ɗaukacin 'yan Najeriya da su dawo cikin hayyacinsu kuma hukumar a shirye take ta amsa musu tambayoyin abinda ya shige musu duhu.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Tayar Masa Da Hankali Lokacin Zabe

Da yuwuwar Tinubu ya naɗa ƴan adawa a gwamnatinsa

A wani labarin na daban mun haɗa muku Jerin Sunayen Jiga-Jigan Jam'iyyun Adawa da Tinubu Zai Naɗa Bayan Rantsarwa da Dalilai.

Ana ganin Tinubu zau ɗauko mutanen ya basu muƙamai a gwamnatinsa sabida gudummuwar da suka ba shi da kuma ƙoƙarinsa na haɗa kan ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262