Mazauna Unguwar Kurmin Kogi Sun Koka Kan Rashin Wuta Na Tsawon Shekaru 8 a Kaduna
- Mazauna wata unguwa da ke karamar hukumar Ikara sun koka kan rashin wutar lantarki har na tsawon shekaru takwas
- Matsalar ta fara ne tun a shekarar 2015 yayin wani ruwa kamar da bakin kwarya da aka tafka a yankin
- Da aka tuntubi hukumar ba da wutar lantarki ta jihar, ta ce ba su taba jin wannan matsalar ba sai a yanzu
Jihar Kaduna - Mazauna Dan Lawal da ke unguwar Kurmin Kogi a karamar hukumar Ikara ta jihar Kaduna sun koka kan yadda suka shafe shekaru takwas babu wutar lantarki.
Matsalar ta fara ne tun shekarar 2015 lokacin da aka yi ruwa kamar da bakin kwarya wanda ya yi sanadiyar lalacewar wutar yankin.
Punch ta tattaro cewa bayan rashin wuta da yankin ke fama da shi, barayi sun kuma fasa cikin na’urar ba da wuta na yankin suka sace manya-manyan wayoyi a ciki.
Kokarin gyara da kuma dawo da wutar ya ci tura bayan shekara takwas ana fama da rashin wutar wadda ya yi sanadiyar gurgunta harkokin kasuwanci a yankin, da yasa jama’a da dama suka kauracewa yankin don gudanar da kasuwancinsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rabonmu da ganin lantarki tun 2015
Wani mazaunin yankin, Yunusa Dan Mairo ya bayyana cewa rabonsu da ganin wuta tun shekarar 2015, matashin ya ce duk kokarin da aka yi don ganin an gyara wutar abin ya ci tura.
Yayin da yace shugabannin yankin sun sha kai korafi ga ‘yan siyasa amma duk a banza, cewar Glitters Online.
A cewarsa:
“A shekarar 2015 an yi wani ruwan sama mai karfi da ya lalata dukkan na’urorin wutar lantarkin da kuma wayoyin da suke dauke da wuta, sannan barayi kuma suka sace manya-manyan wayoyin da suke ciki.
Dangote Ya Bayyana Abin Da Buhari Ya Fada Masa Lokacin Da Ya Yi Niyyar Watsar Da Aikin Matatar Mansa
“Rashin wutar lantarki ya gurgunta harkokin kasuwancinmu musamman masu nika da walda da aski da kuma masu wanki da guga.
“Sauran sun hada da masu kera kofofi da tagogi wanda tuni suka yi hijira zuwa garuruwan makwabta don ci gaba da kasuwancinsu."
Hukumar ba da wutar lantarki ta ce batasan komai game da matsalar ba
Da aka tuntubi shugaban bangaren yada labarai na hukumar ba da wutar lantarki ta jihar Kaduna, Abdullahi Abdulazeez ya ce hukumar su ba ta san da wannan rashin wuta ba, ya ce kamata ya yi unguwar su rubuta zuwa kamfanin don shawo kan matsalar.
A cewarsa:
“Ban taba jin wannan labari ba sai yau, me suka yi akai? Sun rubuta zuwa ga kamfaninmu ko kuma sun tuntubi kamfaninmu akan abin da ya faru? Idan har sun rubuta zan iya ba da martanin da ya dace.
NERC Ta Hana Ma'aikatanta Karɓar Kuɗaɗen Kwastomomin Da Aka Cire Wa Wuta
A wani labarin, hukumar kula da wutar lantarki ta kasa ta gargadi ma'aikatan kamfanin karbar kudi daga hannun kwastomomin da aka yanke wa wuta.
Kamfanin ta fitar da wannan sanarwa ce ta bakin shugaban kamfanin, Sunusi Garba da ya sanya wa hannu.
Asali: Legit.ng