Hotuna: Ɗan El-Rufai, Bello Ya Angwance Da Santaleliyar Amaryarsa a Abuja
- Bello El-Rufai, ɗa a gurin gwamnan Kaduna mai barin gado, Nasir El-Rufai, ya angwance da sabuwar amarya a Abuja
- Bello ne zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai na Kaduna ta Arewa da ya lashe zaɓen ɗan majalisar a zaɓen da ya gabata
- An dai gudanar da auren ne a cikin sirri ba tare da tara jama'a da yawa ko wasu shagulgula ba
Abuja - Bello El-Rufai, ɗan Gwamna Nasir El-Rufai, ya auri Aisha Habibu Shuaibu, diyar tsohon gwamnan jihar Filato da Neja na mulkin soja, Kanal Habibu Shuaibu.
Ma'auratan sun yi auren ne a wani biki na sirri da aka gudanar a Abuja a ranar Juma'a da ta gabata, kamar yadda yake a rahoton Daily Trust.
Aisha ‘yar kasuwa ce da ke gudanar da sana’o’in ta da dama, a yayin da Bello kuma shi ne zaɓaɓɓen ɗan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilai.
Da Dumi-Dumi: Jam'iyyar Labour Ta Dauki Matakin Hambarar Hukuncin Kotun Kano Na Soke Takarar Gwamnan Abia
Haka nan kuma Bello shi ne mai taimakawa zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a wa'adinsa da ya yi a majalisar dattawa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bello ya dora a shafinsa na Fesbuk
Bello El-Rufai ya ɗora wani daga cikin hotunan ɗaurin auren a shafinsa na Fesbuk tare, da sanya alamar zobe da ke nuni da cewa ya yi aure.
Za a yi shagulgulan auren ne tare da sauran abubuwa zuwa nan gaba.
Wannan dai ba shi bane auren Bello na farko ba, domin kuwa a shekarar 2015, Bello ya auri wata mata mai suna Kamilah.
Duba hotunansu a ƙasa:
Mutane da dama da suka haɗa da 'yan uwa da abokan arziƙi sun taya angon murnar wannan ɗaurin aure nasu a shafin sada zumunta na Fesbuk. Ga abinda wasu daga cikinsu ke suke cewa:
Abdullahi Abubakar Salisu cewa ya yi:
Masha Allah, Juma'at Mubarak iyayenmu, gwamna mai jiran gado, mai barin gado, da kuma dan uwanmu, shugaba, mai hidima kuma wakilin al'umma, mamba Kaduna ta Arewa, Mallam Bello El-Rufai jika Hanta.
Allah ya kara mana ladabi da biyayya, Allah yasa albarka.
Rahinat Shuaibu kuma ta ce:
Ina taya ka murna, Oga Bello
Yahaya Jamfalan ya ce:
Allah ya baku zaman lafiya da zuriya mai Albarka.
Bilkisu Abdullahi kuma cewa ta yi:
Masha Allah
Allah ya Baku zaman lafia da zuri’a dayyib
Muh'd Usman Iliyasu ma ya ce:
Ango Hon. Bello El-Rufai Allah ubangiji yabada zaman lafiya!
Zan iya rantsewa cewa ban saci ko kobo ba, cewar El-Rufai
A wani labari namu na baya, gwamnan Kaduna mai barin gado Malam Nasir El-Rufai ya ƙalubalanci tsofaffin gwamnoni kan cewa su zo su yi rantsuwa idan ba su taɓa satar kuɗin jihar ba a wa'adin mulkinsu.
El-Rufai ya yi wannan batu ne a yayin da yake maida martani ga wasu da ke sukarsa kan sha'anin gudanar da mulkinsa.
Asali: Legit.ng