Farfesan Geology Na Farko a Nahiyar Afirika Ya Rigamu Gidan Gaskiya
- Farfesan ilimin binciken kasa da duwastu (Geaology) na farko a faɗin nahiyar Afirka, Mosobalaje Olaloye Oyawoye, ya kwanta dama
- Marigayin, ɗan salin jihar Kwara, ya mutu yana da shekaru 96 a duniya ranar Litinin 22 ga watan Mayu, 2023
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazak ya aike da sakon ta'aziyya ga mutanen ƙaramar hukumar Offa, ya ce Najeriya ta yi babban rashi
Farfesa Mosobalaje Olaloye Oyawoye (CON), mutum na farko da ya taka matsayin Farfesa a fannin ilimin binciken ƙasa (Geology) a nahiyar Afirka ya riga mu gidan gaskiya.
Gwamnatin jihar Kwara ce ta tabbatar da mutuwar Farfesan a wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Litinin 22 ga watan Mayu, 2023, Punch ta ruwaito.
Jaridar Tribune ta rahoto sanarwan na cewa marigayin, yariman Offa, ya mutu yana da shekara 96 a duniya.
A zamanin rayuwarsa, ya yi aiki a matsayin malamin jami'ar Ibadan daga 1960 zuwa 1977. An ba shi matsayin Farfesa a 1966 yana da shekaru 39 a duniya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Farfesan Geology na farko a nahiyar Afirka ya yi aiki a matsayin shugaban hukumar shirya jarabawar fita daga Sakandire a Afirika ta yamma (WAEC).
Gwamnan Kwara ya yi ta'aziyya
Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na jihar Kwara ya aike da saƙon ta'aziyya ga al'ummar ƙaramar hukumar Offa da kuma ɗaukacin mutanen jihar Kwara bisa wannan babban rashi.
A wata sanarwa da Sakataren watsa labaran gwamna, Rafiu Ajakaye, ya fitar, AbduRazak, ya ƙara da cewa mutuwar dattijon ƙasa ba rashi bane na Kwara kaɗai, Najeriya ce ta yi rashi.
Ya ce marigayi Farfesan na ɗaya daga cikin manyan mutanen da ba za'a taɓa mance wa da su ba a tarin ƙasar nan kuma mutum ne da jihar Kwara ke alfahari da shi.
A cewar gwamna AbdulRazak, rasuwar Farfesa Mosobalaje Olaloye Oyawoye, ta kawo ƙarshen nasararon da yake kawo wa ɓangaren ilimi, da taimakon al'ummarsa.
Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Ƙarar da APC Ta Kalubalanci Zabaɓben Gwamnan PDP
A wani rahoton kun ji cewa Kotun zabe a jihar Ribas ta kori ƙarar jam'iyyar APC ta shigar, inda ta kalubalanci nasarar PDP a zaben gwamna.
Lauyan APC ne ga nemi Kotu ta ƙori karar a zaman yau Litinin bayan wata hayanuya ta auku tsakanin ƙauyoyin APC.
Asali: Legit.ng