Gwamna El-Rufa'i Ya Tsige Sarakuna 2 Da Hakimai 3 A Jihar Kaduna
- Gwamnan Kaduna ya tunbuke Sarakuna biyu da Hakimai uku daga kan karagar mulki bisa kama su da aikata laifuka
- Malam Nasiru El-Rufai ya umarci Masarautun Piriga da Arak su fara shirin bin matakan da ya dace domin naɗa sabbin Sarakuna
- Wannan mataki na zuwa ne mako ɗaya tal gabanin El-Rufa'i ya sauka daga kujerar gwamnan Kaduna
Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya hamɓarar da Sarakuna biyu daga kan karagar mulki mako ɗaya gabanin wa'adinsa ya ƙare.
Punch ta rahoto cewa Malam Nasiru ya tsige rawanin Sarkin Piriga, Mai martaba Jonathan Paragua Zamuna, da kuma basaraken masarautar Arak, mai martaba Aliyu Iliyah Yammah.
Kwamishinar kula da harkokin ƙananan hukumomi a Kaduna, Hajiya Umma Ahmad, ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin 22 ga watan Mayu.
Ta ce Sarakunan biyu za su sauka daga kan karagar mulki daga yau Litinin 22 ga wata kuma wannan mataki ya biyo bayan shawarin ma'aikatar kananan hukumomi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwamishinar ta ce:
"Hakimin Garun Kurama, Babangida Sule, zai riƙe masarautar Piriga har zuwa lokacin da za'a naɗa sabon sarki. Mun umarci Magatakardan masarautar ya fara bin matakan zaƙulo wanda za'a naɗa."
"Haka nan Magatakardan Masarautar Arak, Gomna Ahmadu, zai kula da harkokin masarautar kuma ya fara shirye-shiryen bin matakan naɗa Sabon basarake."
Meyasa El-Rufai ya tsige Sarakunan biyu?
A rahoton Daily Trust, Sanarwan ta ƙara da cewa:
"Gwamnatin El-Rufai ba ta gamsu da bayanan Aliyu Iliyah Yammah ba game da tuhumar naɗa hakimai huɗu da ya yi saɓanin guda ɗaya tal da aka sahale masa ya naɗa kuma ba ya zama a Masarautar Arak kwata-kwata."
"An hamɓarar da mulkin Jonathan Paragua Zamuna ne biyo bayan rikicin da ya ɓarke kwanan nan tsakanin yankunan Gure da Kitimi, Masarautar Piriga a ƙaramar hukumar Lere kuma ba ya zama a gida."
Daga karshe kwamishinar ta sanar da tsige Dagacin Aban, takwaransa Abujan Mada da kuma Dagacin Anjil duk a karkashin Masarautar Arak.
Zamu ɗauki dubbannin yan Najeriya aiki - Ɗangote
A wani rahoton na daban kun ji cewa Sabuwar Matatar Man Dangote Zata Samar da Ayyuka Ga Yan Najeriya.
Da yake jawabi a wurin taron kaddamarwa ranar Litinin, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ve sabuwar matatar zata samar dumbin guraben ayyukan yi ga matasan Najeriya.
Asali: Legit.ng