Matatar Dangote: Ina Farin Ciki Don Zan Bar Najeriya Hannun Jajirtattu, Buhari
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da matatar man Dangote wacce itace irinta mafi girma a duniya, a Legas ranar Litinin
- Buhari ya yabawa Aliko Dangote kan zuba hannun jari a matatar, ya kuma shawarci sauran 'yan kasuwa da su yi koyi da shi
- Buhari ya kuma ce yana da yaƙinin cewa magajinsa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai ci gaba da inganta harkokin tattalin arziki da kasuwanci a kasar
Legas - Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar Litinin ya ce ya yi farin ciki da barin tattalin arziƙin Najeriya a hannun ƙwararru.
Shugaban mai barin gado ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi a wajen ƙaddamar da matatar man Dangote a Legas, Vanguard ta yi rahoto.
Buhari ya ce Tinubu zai ci-gaba da inganta tattalin arziƙin ƙasa
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Wannan babbar masana’anta da muke ƙaddamarwa a yau misali ce ƙarara na abin da za a iya samu idan aka ƙarfafawa ‘yan kasuwa gwiwa da tallafa musu da kuma idan aka samar da yanayin da mutane za su iya saka hannun jari don ci-gaban kasuwanci."
Buhari ya ƙara da cewa ya na kyautata zaton cewa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar mai jiran gado zai cigaba da yin abubuwan da za su taimaki tattalin arziƙin ƙasa
A faɗarsa:
“Ina da yaƙinin cewa mutumin da zai gaje ni, mai girma Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai ci gaba da inganta tattalin arziƙinmu da kasuwancinmu, tare da bin tsarinmu na ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa don ƙara haɓɓaka tattalin arziƙinmu da bunkasa shi cikin gaggawa.”
"Na yi farin cikin barin tattalin arzikinmu a hannun kwararru."
Buhari Ya Buƙaci sauran ‘yan kasuwa da su zuba jari a Nijeriya
Da ya ke bai wa sauran ‘yan kasuwa maza da mata shawara kan su yi ƙoƙarin bin matakan da Dangote ya bi, Buhari ya ce:
“Ina kira da ƙarfafa gwiwar sauran manyan ‘yan kasuwanmu da su yi koyi da wannan fitaccen ɗan kasuwan, su haɗa hannu da gwamnati wajen ƙara haɓɓaka ci gabanmu domin tabbatar da ƙarfin tattalin arzikin da ake kallon ƙasarmu da shi a duniya.”
"Lokacin da na zagaya Afirka kuma na haɗu da 'yan'uwana shugabannin ƙasashe (kuma naji daɗi wasunsu suna nan wurin), sau da yawa nakan ji a raina cewa ƙasarmu na da albarkatu da jarin ɗan adam domin jagorantar haɓaka tattalin arzikin Afrika, cigaba da kuma cimma burin 2063, na 'Afrikar da dukanninmu ke so.'”
Ana dai sa ran wannan matatar mai za ta rika samar da akalla gangar mai 650,000 a kowace rana, The Nation ta yi rahoto.
Dalilin da ya sa na tsunduma kasuwancin man fetur
A wani labari namu na baya, shugaban rukunin kamfanoni na Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilin da ya sa ya shiga kasuwancin mai.
Ya bayyana wa manema labari dalilansa da dama, ciki hadda matsalar da ya samu a shekarar 2007, lokacin da ya yi yunƙurin shiga harkar kasuwancin na man fetur.
Asali: Legit.ng