Matatar Man Dangote: Dalilin Da Ya Sa Muka Shiga Harkar Mai, Dangote Ya Yi Bayani

Matatar Man Dangote: Dalilin Da Ya Sa Muka Shiga Harkar Mai, Dangote Ya Yi Bayani

  • Shugaban rukunin kamfanoni na Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa ɓangaren kayan noma ba ya cin kuɗaɗe da yawa sosai
  • Ya ce hakan ta sanya suka karkatar da akalar kuɗaɗen da suke samu zuwa ɓangaren harkokin kasuwancin mai
  • Dangote ya ce ba dole sai a harkokin mai mutum zai yi kuɗi ba kamar yadda mutane da dama ke tunani

Lagos - Shugaban rukunin kamfanoni na Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya bayyana dalilin da ya sanya shi tsunduma kasuwancin mai.

A wata hira da jaridar Vanguard, attajirin ya yi bayani kan abinda ya ja hankalinsa har ya yanke shawarar shiga kasuwancin na mai.

Shekaru goma sha ɗaya, a jere, ya kasance mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka kamar yadda yake a mujallun Forbes da Bloomberg.

Kara karanta wannan

Mulki Dadi: Shugaba Buhari Ya Bayyana Muhimmin Abinda Zai Yi Kewa Sosai Bayan Ya Koma Daura

Dangote
Dangote Ya Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ya Shiga Harkar Mai. Hoto: @dangote
Asali: Twitter

Dangote wanda ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar Al-Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar, ya fara sana’arsa ne a shekarar 1978.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya fara da sana’ar shinkafa, sikari da siminti kafin daga bisani shi ma ya fara samar da kayayyakin masarufi.

Kamfanin Dangote yanzu haka yana aiki a ƙasashen Afirka 17 kuma shi ke kan gaba a kasuwar siminti a nahiyar.

Dangote ya bayyana cewa aikin da suka yi wajen tabbatar da gina matatar man ba ɗan ƙarami ba ne, kuma an ɗauki lokaci ana shiryawa hakan.

Me yasa Dangote ya faɗa harkar mai, Aliko Dangote ya yi bayani

Dangote ya ce burinsa shine ya gina babban kamfani wa 'yan Afrika. Ya ce ya lura da an fi mayar da hankali a ɓangaren noma, wanda shi kuma baya cin kuɗaɗe da yawa.

Kara karanta wannan

Dala $800m: Majalisar Tarayya Ta Amince Wa Shugaba Buhari Ya Ƙara Sunkoto Bashi Bisa Sharadi 1 Rak

Ya ƙara da cewa a shekarar 2015, ya tsaya ya yi tunanin inda ya kamata ya zuba kuɗaɗensa na ribar da kamfanoninsa ke samu.

Dangote ya ce ya lura da cewa duk da kuɗaɗen da ya kashe a kamfaninsa na taki, yana da ragowar kuɗaɗe masu yawa.

Daga nan ne ya yanke shawarar tsunduma harkar mai, wacce dama ya taɓa yunkurin yi a shekarun baya.

Ba dole sai kana harkar mai za ka samu kuɗaɗe ba

Dangote ya kuma ce duk da dai mutane da dama sunyi kuɗi ta hanyar kasuwancin mai, amma shi bai taɓa jaraba ta ba, wanda hakan ke nuni da cewa ba dole sai a mai mutum zai samu kuɗi ba.

A cewarsa:

“Da yawa daga cikin mutane sun samu kuɗinsu ne ta hanyar mai. Amma ba mu taɓa shiga harkar ta mai ba, wanda hakan ke tabbatar da cewa ba lallai sai mutum ya shiga harkar mai ba. A Najeriya man fetur ya lalata mana tunani. Kowa kawai yana magana ne akan mai, mai, mai, mai.”

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Da Ya Lashi Takobin Yaƙar Tinubu a Majalisa Ta 10 Ya Gana da Buhari, Bayanai Sun Fito

Dalilin da ya sa ban shiga kasuwancin mai tun a baya ba

Dangote a ci gaba da bayaninsa ya ce, abinda ya hana ya shiga hidimar a baya, shine ganin yadda rashawa ta yi yawa a ɓangaren, ta yadda ake kallon waɗanda ke ɓangaren a matsayin 'yan rashawa.

Ya ƙara da cewa ba ya so mutane su riƙa masa irin wannan kallon. Sannan ya ce akwai buƙatar mutum ya yi karatun abu kafin ya shiga cikinsa.

Ya ce a shekarar 2007, sun sayi matatun mai guda biyu da gwamnati mai barin gado ta siyar, sai dai da sabuwar gwamnati ta zo, ta ce ba ta san da batun ba.

Allah ya nufi zan yi matata ta

Ya ce tun daga wannan lokaci ne ya ƙudiri aniyar gina tasa matatar. Sai dai bai samu damar farawa ba sai a shekarar 2015.

Matatar man ta Dangote na nan a Ibeju-Lekki da ke Legas. Ma'aikata ce mai faɗi da ta kai hekta 2,635.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: "Shugaban EFCC Ya Nemi Cin Hancin $2m Daga Wuri Na," Gwamnan APC Ya Fasa Ƙwai

An bayanna cewa matatar za ta iya samar da wutar lantarki a jihohi biyar da suka haɗa da Oyo, Ogun, Osun, Kwara da Ekiti.

Irin man da matatar za ta samar

Sannan kuma ana sa ran wannan matata za ta riƙa samar da duka man da ake buƙata domin amfani da shi a Najeriya, wato lita miliyan 53 na fetur a kowace rana da lita miliyan 34 na dizel a rana.

Haka nan kuma, kamfanin zai riƙa samar da lita miliyan 10 na kalanzir a rana. Sannan kuma akwai man jirgi da sauransu. Kamfanin zai kuma samar da rarar kowane ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa don fitarwa waje.

Jaridar This Day ta ruwaito cewa akalla shugabannin kasashe bakwai ne za su halarci bikin bude wannan matatar man ta Dangote.

Harkallolin kasuwanci tara da Abdulsamad BUA ke da su

A wani rahoton mu na daban, mun kawo muku harkokin kasuwanci guda tara da attajirin dan kasuwar nan Abdulsamad Isiyaka Rabiu ke da su.

Attajirin wanda ya na cikin jerin mutane 10 da suka fi kowa kudi a Afrika na gaba-gaba wajen harkokin kayan masarufi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng