'Yan Bindiga Sun Halaka Manoma Mutum Tara a Jihar Kaduna
- Ƴan bindiga sun farmaki manoma suna tsaka da aiki a gonakin su a Unguwar Danko cikin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna
- Mummunan harin na ƴan bindigan ya yi sanadiyyar halaka manoma tara, yayin da wasu da dama suka raunata
- Gwamnatin jihar Kaduna ba ta ce komai ba dangane da harin wanda ya yi sanadiyyar salwantar rayukan mutane da dama
Jihar Kaduna - Aƙalla manoma tara ƴan bindiga suka halaka a Unguwar Danko kusa da ƙauyen Dogon Dawa, a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a ranar Asabar da rana, lokacin da manoman suke aiki a gonakinsu.
Mazauna yankin sun kuma bayyana cewa ƴan bindigan sun yi awon gaba da wasu manoma mutum uku, zuwa wani waje wanda ba a san ko ina ne ba.
Zaɓaɓɓen ɗan majalisa mai wakiltar Kakangi, Yahaya Musa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa dukkanin waɗanda aka halaka manoma ne, sannan waɗanda suka samu raunika an garzaya da su zuwa asibiti domin duba lafiyarsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A kalamansa:
"Eh tabbas an tabbatar min da hakan ranar Lahadi da safe cewa ƴan bindiga sun halaka manoma tara a Unguwar Danko kusa da ƙauyen Dogon Dawa, ranar Asabar da rana sannan wasu daban kuma sun samu raunika."
Ya kuma yi bayanin cewa wasu daga cikin mutanen ƙauyen sun yi fito na fito da ƴan bindigan, wanda hakan ya sanya wasu daga cikinsu suka samu raunika.
Hukumomi ba su ce komai ba dangane da harin
Har ya zuwa yanzu gwamnatin jihar Kaduna ba tace komai ba dangane da lamarin, cewar rahoton The Punch.
'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Jami'an Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa, Sun Aiko da Sako Mai Ta Da Hankali
Sai dai kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya yi alƙwarin zai bayar da cikakkun bayanai idan sun samu.
Jikan Sarki Ya Kubuta Daga Hannun 'Yan Bindiga
A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa jikan sarkin Kagarko a jihar Kaduna, ya kuɓuto daga hannun miyagun ƴan bindiga.
Ƴan bindiga dai sun je har fadar sarkin na Kagarko, inda suka yi awon gaba da wasu ƴaƴansa da jikokinsa.
Asali: Legit.ng