Kana Naka: Adenuga Ya Yi Kasa a Jerin Attajirin Duniya Bayan Ya Yi Asarar Sama da N230bn Cikin Kwanaki 20

Kana Naka: Adenuga Ya Yi Kasa a Jerin Attajirin Duniya Bayan Ya Yi Asarar Sama da N230bn Cikin Kwanaki 20

  • Dukiyar Mike Adenuga ta yi kasa da $500m a cikin kwanaki 20 kacal, wanda hakan ya shafi matsayinsa a jerin attajiran duniya
  • Wannan sauka da ya yi na da nasaba da yadda harkallarsa ta dan yi tsami a ‘yan kwanakin baya-bayan nan, inji rahoto
  • Duk da asarar da ya tafka, har yanzu Adenuga na daga cikin manyan attajiran Najeriya da ma Afrika kamar yadda aka saba

Mike Adenuga, attajirin dan Najeriya mai harkallar sadarwa da kuma mai ya ga raguwar arziki cikin kwanakin baya.

A cewar rahoton Forbes, dukiyar Adenuga ta fadi da $500m, kwatankwacin N230.5bn a tsakanin 1 zuwa 20 ga watan Mayun bana.

As of Sunday, May 21, 2023, Adenuga's net worth stands at $5.6 billion, compared to $6.1 billion on May 1, 2023.

Ya zuwa ranar Lahadi, 21 Mayu, 2023, dukiyar Adenuga bata wuce $5.6bn ba, idan aka kwatanta da na 1 ga watan Mayu; $6.1bn.

Kara karanta wannan

A sharar titi: Yadda wata mata ke hada sama da N860k a sana'ar shara

Yadda Adenuga ya ga ragi a duniyarsa
Mike Adenuga, attajirin dan Najeriya | Hoto: Daily Post Nigeria
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Faduwar da ya samu, ya shafi matsayinsa a jerin attajiran duniya, inda ya sauka daga na 429 a farkon Mayu zuwa na 481 a ranar 21 ga watan Mayu.

Tangal-tangal a dukiyar Adenuga

A farkon 2023, Adenuga ya dan farfado bayan shan fama da tangal-tangal na hawa da saukar dukiyarsa a 2022, amma hakan ya dawo a cikin 2023.

A ranaku 26 na farko a 2023, dukiyarsa ta karu da $600m, inda jumillar kudin suka tashi daga $5.6bn zuwa $6.2bn.

Duk da haka, Adenuga na daga cikin attajiran Najeriya da ma nahiyar Afrika da ke kan gaba a jerin attajiran.

Baya ga kasancewarsa daya daga cikin uku na attajiran Najeriya a kundin Forbes, mujallar ta kuma ambace shi cikin attajiran nahiyar Afrika.

Harkallolin kudi na Adenuga

Adenuga ya samu kudadensa ne ta hanyar zuwa jari a fannin sadarwa da kuma man fetur da dai sauran harkallolin da ba a rasa ba.

Kara karanta wannan

Dalilai 6 Da Za Su Wargaza Hukuncin Kotun Kano Na Soke Takarar Alex Otti, Fitaccen Lauya Ya Magantu

Kari kan harkallarsa ta sadarwa karkashin kamfanin Globacom Limited da Conpetro Limited, Adenuga ne mai kaso 74.4% na Conoil Plc.

Conoil dai sanannen kamfanin man fetur da sauran albarkatun makamashi ne a Najeriya.

Harkallolin Abdulsamad guda 9 a Najeriya

A bangare guda, rahoto ya bayyana irin harkallolin da attajirin Najeriya dan asalin jihar Kano ke yi a tsawon shekaru yanzu.

Abdulsamad, shine mai kamfanin BUA Group da ke samar da siminti, abinci da sauran amfanin yau da kullum a Najeriya da ma kasashen makwabta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.