'Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an 'Yan Sanda Biyu a Jihar Imo

'Yan Bindiga Sun Halaka Jami'an 'Yan Sanda Biyu a Jihar Imo

  • Ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari kan jami'an ƴan sanda da ke bakin aikin su a jihar Imo
  • Ƴan bindigan sun halaka jami'an ƴan sandan mutum biyu a farmakin da suka kai musu a wajen shingen binciken su
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda tace ta bazama farautar miyagun domin cafke su

Jihar Imo - Ƴan bindiga sun halaka jami'an ƴan sanda biyu akan kwanar Ngor Okpala, cikin ƙaramar hukumar Ngor Okpala ta jihar Imo, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Ƴan bindigan waɗanda ake zargin mambobin haramtacciyar ƙungiyar Eastern Security Network (ESN) ne, ɓangaren da ke ɗauke da makamai na ƙungiyar Indigenous Peoples of Biafra (IPOB), sun farmaki ƴan sandan ne a wajen shingen binciken su a yankin.

'Yan bindiga sun halaka jami'an 'yan sanda biyu a jihar Imo
Usman Alkali Baba, babban sufeto janar na 'yan sanda Hoto: Guardian.com
Asali: UGC

Biyu daga cikin jami'an waɗanda ke aiki da sashin daƙile ta'addanci (CTU), sun halaka nan take a wajen, yayin da ƴan bindigan suka ranta a na kare.

Kara karanta wannan

Tsugunne Ba Ta Kare Ba: 'Yan Sanda Sun Gabatar Da Muhimman Bayanai Kan Tuhumar Alhassan Doguwa

Wannan harin na zuwa ne wata ɗaya bayan an halaka ƴan sanda biyar a wajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Henry Okoye, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya tabbatar da cewa jami'an ƴan sandan sun yi musayar wuta da maharan kafin su arce zuwa cikin daji, cewar rahoton Sahara Reporters.

A kalamansa:

"Eh tabbas jami'an ƴan sandan mu mutum biyu sun halaka. Ƴan bindiga ne suka kai musu farmaki waɗanda ake zargin mambobin ƙungiyar Eastern Security Network, (ESN) ɓangaren da ke ɗauke da makamai na ƙungiyar Indigenous Peoples of Biafra (IPOB)."
"Jami'an mu sun fafata da su inda suka gudu zuwa cikin daji suka bar motar su. Bayan mun ƙwato motar mun same ta cike da jini, wanda hakan ya nuna sun samu raunika."
"Yanzu haka muna farautar su a Ngor Okpala domin cafke su, tun da mun yi amanna cewa sun samu munanan raunika."

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Bazama Aiki, Sun Cafke Wasu Masu Hannu Kan Kisan Jami'an Amurka a Najeriya

Ya kuma nemi ma'aikatan lafiya da asibitoci da su sanya ido sosai, sannan su kai musu rahoton duk wani wanda ya zo wajen su ɗauke da munanan raunika.

Sojoji Sun Kai Samame Mafakar Yan Bindiga a Zamfara

A wani rahoton na daban kuma, dakarun sojoji sun ragargaji ƴan bindiga a jihar.Zamfara, a wani sumame da suka kai musu maɓoyar su.

Dakarun sojojin sun samu nasarar tura da dama daga cikin ƴan bindigan inda idan aka je ba a dawowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng