Yan Sanda Sun Yi Nasarar Kwamushe Barayin Waya Bayan Sun Fasa Shago a Jihar Katsina
- Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina sun kama wasu da ake zargin sun fasa shago da satar wayoyi 48
- Kakakin rundunar, CSP Gambo Isah shi ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a 19 ga watan Mayu da muke ciki
- An kama wadanda ake zargin su biyu Ibrahim Sani mai shekaru 22 da kuma Abubakar Haruna mai shekaru 23 a ranar Juma’a
Jihar Katsina - Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kama wasu da ake zargi da fasa shaguna tare da satar wayoyin hannu guda 48.
Kakakin rundunar a jihar, CSP Gambo Isah shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a 19 ga watan Mayu a Katsina.
Isah ya ce wadanda ake zargin su biyu, Abubakar Haruna mai shekaru 23 da Ibrahim Sani mai shekaru 22, an kama su ne a ranar Laraba 17 ga watan Mayu, cewar jaridar Daily Nigerian.
Matasan an kama su ne a wani shagon mai siyar da wayoyi a Tsohuwar Tasha a cikin birnin Katsina inda suka saci wayoyi 48 a cikin shagon.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Punch ta tattaro cewa an kama matasan ne bayan samun bayanan sirri inda aka tabbatar cewa yaran sun hada baki da wani mai suna Tayi wanda har yanzu ba a san inda yake ba.
Matasan sun tabbatar da aikata laifin da ake tuhumarsu akai
Dukkan wadanda ake zargin sun tabbatar da aikata laifin da ake tuhumarsu akai inda suka kara da cewa sun gama tsara yadda za su siyar da wayoyin a kasashe makwabtan Najeriya.
‘Yan sanda sun ba da tabbacin kama wadanda ake zargin
Kakakin ya ce jami’an ‘yan sanda yanzu haka sun bazama neman daya wanda ake zargin sun hada kai da shi wurin tafka wannan ta’asar inda ya tabbatar cewa za su kama duk masu hannu a aikata hakan kuma a hukunta su dai-dai da laifinsu kamar yadda doka ta tanadar.
Jami'an Yan Sanda Sun Yi Nasarar Sheke Kasurgumin Dan Bindiga a Jihar Kaduna
A wani labarin, rundunar 'yan sandan jihar Kaduna sun yi nasarar hallaka wani kasurgumin dan bindiga da ya addabi yankin.
Rundunar ta ce bayan nasarar hallaka shin, jami'anta sun kwato babur daga hannun dan bindigan da suke amfani da shi.
Asali: Legit.ng