Hawaye, Bakin Ciki Yayin Da Wanda Ya Kafa FCMB Ya Rasu, Bayanai Sun Fito
- Shugaban bankin FCMB kuma wanda ya assasa ta Otunba Balogun ya rasu bayan ya yi bikin ranar zagayowar haihuwarsa
- Balogun kafin rasuwarsa shi ne ke rike da sarautar Asiwaju na Kiristocin Ijebu ya rasu yana da kimanin shekaru 89 a duniya
- Mutuwar shahararren dan kasuwan wanda aka haife shi a jihar Ogun na zuwa ne watanni biyu bayan ya yi bikin ranar haihuwarsa
Abuja - Shahararren dan kasuwa Otunba Olasubomi Balogun wanda ya kafa bankin First City Monument Bank (FCMB) ya riga mu gidan gaskiya.
Shahararren dan kasuwan wanda ya yi bikin ranar haihuwarsa a watan Maris na wannan shekara, ana hasashen cewa ya mallaki dukiyar da ta kai $700m.
Jaridar Legit ta tattaro cewa dan kasuwan ya mutu ne a birnin London a ranar Juma’a 19 ga watan Mayu.
Mista Balogun an haife shi a Ijebu da ke cikin jihar Ogun, ya kasance mutum mai kima a idon jama’a da ya ke son ci gaban al’umma.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Meye mukamansa?
Otunba Michael Olasubomi Balogun kafin rasuwarsa shi ne yake rike da sarautar Asiwaju na Kiristocin Ijebu, cewar jaridar Daily Independent .
Shi ne ya kafa bankin FCMB sannan kuma shi ne shugabanta wanda aka misalta da mutum mai karimci da son jama’a.
Ya kasance a kullum burinshi shi ne ya ga al’umma ta ci gaba, sannan kuma ya kasance kullum a cikin bautar ubangijinsa.
Balogun ya bayyana yadda yake rayuwarsa.
Jaridar Punch ta tattaro cewa, Balogun ya taba bayyana yadda yake gudanar da rayuwarsa inda ya tabbatar cewa ba zai taba kaucewa daga hanyar bin ubangijinsa ba.
A cewarsa:
“Ni dan Allah ne, kuma ubangiji yana tausaya min. Duk abin da ka gani a tare da ni to daga ubangiji ne. Don meyasa zan kauce daga ayyuka masu kyau.”
Alkalin Babbar Kotun a Kwara, Oyinloye, Ya Riga mu Gidan Gaskiya Yana da Shekara 58
A wani labarin, alkalin kotu dake zamanta a jihar Kwara Sikiru Adeyinka Oyinloye ya riga mu gidan gaskiya a ranar Lahadi 23 ga watan Afrilu na wannan shekara.
Marigayi mai shari'an Sikiru Adeyinka ya rasu ne bayan fama da jinya da ya shafi wuyansa na tsawon lokaci.
Asali: Legit.ng