Tsohuwar Ministar Ilmi Ezekwesili, Ta Nemi Buhari Ya Sauka Ya Miƙa Mataa Mulkin Ƙasar Nan

Tsohuwar Ministar Ilmi Ezekwesili, Ta Nemi Buhari Ya Sauka Ya Miƙa Mataa Mulkin Ƙasar Nan

  • Tsohuwar ministar ilimi, Obiageli Ezekwesili, ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta miƙa mata mulki
  • Ezekwesili ta bayyana Buhari a matsayin babban Kwamandan askarawan Najeriya mara kuzari
  • Ezekwesili ta wallafa haka a shafinta na Tuwita ne biyo bayan korafe-korafen da magoya bayan shugaban kasar suka yi kan gazawarsa wajen tabbatar da tsaron kasa da ‘yan kasar

Tsohuwar ministar ilimi, Obiageli Ezekwesili, ta buƙaci shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya miƙa mata ragamar mulkin ƙasar nan cikin gaggawa.

Ezekwesili ta bayyana hakan ne yau Laraba, a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na sada zumunta a Tuwita.

A cikin saƙon, ta bayyana Buhari a matsayin "babban Kwamandan askarawan Najeriya mara kuzari."

Buhari Ezek
Tsohuwar Ministar Ilmi Ezekwesili, Ta Nemi Buhari Ya Sauka Ya Miƙa Ma Ta Mulkin Ƙasar Nan. Hoto: Tribune, The Eminent Leaders
Asali: UGC

Ƙorafin magoya Buhari ne ya sanya ta wallafa rubutun

Saƙon na ta ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da magoya bayan shugaba Buhari suka yi, kan rashin iya tsare ƙasar da shugaban ya yi.

Kara karanta wannan

Buhari Na Iya Bakin Ƙoƙarinsa Wajen Magance Matsalar Hauhawar Farashi a Najeriya, Cewar Garba Shehu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tsohuwar ministar ta ƙara da cewa ta na kuma maraba da kuri'un da magoya bayan Buhari za su kaɗa mata kan hakan.

Ezekwesili ta rubuta:

“Ina kira ga babban kwamandan rundunar sojin Najeriya mara kuzari @MBuhari da ya gaggauta miƙa min ragamar mulki domin gamsar da magoya bayansa da ya gaza tabbatarwa da tsaron ƙasa, ‘yan kasa da ma mazauna Najeriya.
"Ina maraba da goyon bayan da za su nuna a kaina.
"Ina maraba da kuri'ar amincewarsu a gare ni,"

Ƙoƙarin neman ɗaukar wani mataki ba ya da amfani

Ta kuma bayyana cewa a duk lokacin da ta ji tana so gwamnati ta ɗauki mataki kan wani abun sai ta tuna da cewa babu abinda za a yi.

Ta kuma ƙara da cewa:

"Da zarar na fara nazari kan cewa ƙoƙarin neman ɗaukar wani mataki kan al'amuran shugabanci daga gwamnatin @MBuhari daidai ya ke da abin da ba zai yiwu ba, sai kawai na daina.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari Ta Bayyana Abinda Za a Riƙa Tuna Mijinta Da Shi Bayan Ya Bar Mulki

"Muna da wani da ake cewa babban kwamandan askarawan Najeriya, wanda ya durkusar da harkokin tsaron kasarmu ƙarshe mara daraja.”

Buhari ya bayyana abubuwa uku ƙwarara da ya yi

A ragowar 'yan kwanakin da suka ragewa shugaba Buhari a ofis, ya yi jawabi kan wasu nasarori da ya samu a mulkinsa na shekara takwas.

Ya bayyana hakan ne ta hannun sakataren gwamnatin tarayya, Ibrahim Gambari a wani taro a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng