An Hana ’Yan Jaridu da Lauyoyi Shiga Kotun da Ake Sauraron Karar Abba Kyari

An Hana ’Yan Jaridu da Lauyoyi Shiga Kotun da Ake Sauraron Karar Abba Kyari

  • Kotun dake sauraren korafe-korafe akan dan sanda Abba Kyari ta hana ‘yan jaridu da lauyoyi shiga kotun
  • Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ba da wannan umarni bayan lauyan gwamnati ya yi korafi akan hakan
  • A karshe mai shari’a Nwite ya ba da umarnin duk wadanda ba su da alaka da shari’ar su fice daga kotun

Abuja - Kotu ta hana ‘yan jaridu da lauyoyi da kuma sauran jama’a shiga cikin kotun da ake ci gaba da sauraren karar Abba Kyari da ake zargi da safarar kwayoyi, a yau Talata 16 ga watan Mayu a kotun dake zamanta a Abuja.

Mai shari’a Emeka Nwite ne ya ba da wannan sanarwa bayan lauyan dake kare Hukumar Hana Sha da Fataucin Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA) Mista Joseph ya shigar da korafi don kare masu ba da shaida a kotu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Dagaci da Wasu Mutane 3 a Jihar Niger

Abba Kyari/ Kotu
An Hana ’Yan Jaridu da Lauyoyi Shiga Kotun da Ake Sauraron Karar Abba Kyari, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Lauyan ya roki kotun da ta hana sauran lauyoyi da ‘yan jaridu da kuma sauran masu kawo ziyara dake cikin kotun shiga inda ake shari’ar har lokacin da za a kammala.

Daga nan ne Mai shari’a Nwite ya ba da umarnin duk wadanda ba su da alaka da shari’ar su fita daga kotun, cewar jaridar Premium Times.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da ya roki lauyoyin da ba su da alaka da karar Abba Kyari da su yi hakuri da hukuncin na dan lokaci kadan.

'Yan jaridu sun tamabayi lauyan gwamnati akan hukuncin kotun

Da ‘yan jaridu suka tambayi lauyan gwamnati akan wannan hukunci, sai ya ce an umarce shi da ya bai wa wasu daga cikin jami’an da za su ba da shaida a kotun.

Ya ce ya lura da wadansu mukarraban babban sifetan ‘yan sanda da suke tare da Abba Kyari suna zuwa kotun.

Kara karanta wannan

Ku Cika Alkawuran Da Kuka Dauka Ko A Yi Waje Da Ku, Buhari Ya Shawarci Gwamnoni

A cewar lauyan gwamnatin:

“Ba ku san su waye ba ne suke zuwa nan, wannan muna yi ne don kare masu ba da shaida a kotun.

“Yanzu mun kai wani mataki akan shari'ar nan, don ana zargin kaman muna yi wa Abba Kyari bita da kulli ne.”

Babu matsala a kotu

Jaridar Guardian ta tattaro cewa zaman kotun na ci gaba da gudana har lokacin hada wannan rahoto.

Ana zargin Abba Kyari da wasu mutane uku bisa alaka da kwayoyi, sauran mutane ukun sun hada da ACP Sunday Ubia da Sifeta Simon Aririgba da kuma sifeta John Nuhu.

Hodar Iblis: Bidiyon lokacin da Abba Kyari ke bada cin hancin daloli Ya Yadu

A wani labarin, an gano faifan bidiyo a kafar sada zumunta lokacin da Abba Kyari ke karbar daloli a cikin mota.

Ana zargin Abba Kyarin da karbar cin hanci har na $61,500 na hodas iblis da aka siyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.