Buhari Ba Shi da Asusun Banki Ko Daya Dake Shake da Kudin Haram, in Ji Garba Shehu

Buhari Ba Shi da Asusun Banki Ko Daya Dake Shake da Kudin Haram, in Ji Garba Shehu

  • Kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mai gidansa ba shi da asusun banki ko daya na haram
  • Garba Shehu ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels a ranar Talata
  • Ya bayyana yadda shugaban ke jin bakin cikin yadda wadansu masu laifi ke yawo a motoci da jirage

Abuja - Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari akan yada labarai, Mallam Garba Shehu ya bayyana cewa shugaban kasan ba shi da asusun banki guda daya dake dauke da kudin haram.

Shehu ya bayyana mai gidan nasa a matsayin mutum mai kankan da kai inda ya ce har yanzu Buhari yana nan kamar yadda mutane suka sanshi a baya.

Garba Shehu/Buhari
Buhari Ba Shi da Asusun Banki Ko Daya Dake Dauke da Kudin Haram, in Ji Garba Shehu, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Garba shehu ya fadi hakan a wani hira da ya yi da gidan talabijin na Channels ranar Talata 16 ga watan Mayu lokacin da yake bayyana yadda gwamnatinsu ke yaki da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Ku Cika Alkawuran Da Kuka Dauka Ko A Yi Waje Da Ku, Buhari Ya Shawarci Gwamnoni

Ya ce wasu ‘yan siyasa a Najeriya sun kware wurin sata da kuma ajiye kudaden haram a asusun bankunansu na gida da waje musamman lokacin da gwamnatin da suke ciki tazo karshe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

“A matsayi na kakakin shugaban kasa, a kullum ina kwanciya cikin nitsuwa sanin cewa ba wanda zai kira ni daga gida ko a kasashen waje ya ce an binciko wani asusun banki na Buhari mai dauke da makudan kudade na haram.
“Wannan ba halin Buhari ba ne, ya wuce wannan mataki na cin hanci kuma haka zai gama mulkinsa ko rayuwarsa ba tare da cin hanci ba."

Buhari mai shekaru 80 zai kammala wa’adin mulkinsa na biyu ne a ranar 29 ga watan Mayu, yayin da za a rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu a ranar, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Wasu Wurare 4 da Bola Tinubu Zai Iya Shan Wahala Bayan Ya Gaji Muhammadu Buhari

Mutane na korafi dangane da mulkin shugaba Buhari

Mutane da dama suna korafin cewa ba abin da gwamnatin shugaba Buhari ta tsinana ganin yadda cin hanci da rashawa da suke ikirarin hanawa ke kara ta’azzara a kasar.

Hakazalika, wasu na kallon yada matsalar tsaro ta kara ta'azzara a mulkin nasa sabanin yadda ya karbi kasar.

Garba Shehu ya yi bayanin yadda Buhari ke ganin cin hanci a kasar

Da yake maida martani kan tambayarsa da aka yi cewa me yasa cin hanci ke kara yawa a gwamnatinsu duk da ikirarin yakin da suke yi da matsalar, Garba Shehu ya ce:

“Idan ka tambayi Buhari wannan tambaya, zai ce maka shi ma abin ya na bashi mamaki ganin yadda wadanda ake zargin cin hanci suna yawo a motoci masu tsada da jirage maimakon a gidan gyaran hali.”

Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Soki Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

Kara karanta wannan

Yawaita Zuwa Turai: Tinubu zama zai yi ya mulki Najeiya, inji hadiminsa

A wani labarin, kungiyar kabilar Ibo a Najeriya 'Ohanaze Ndigbo' ta caccaki shugaba Buhari kan rashin daukar mataki akan hukuncin Ike Ekweremadu a Burtaniya.

in baku manta ba, kotun Burtaniya a ranar Juma'a ta yanke wa tsohon mataimakin majalisar dattawan hukuncin daurin shekaru 9 da matarsa Beatrice.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.