Ajali Ya Yi Kira: Wani Mutum Ya Mutu Bayan Faɗowa Daga Bishiyar Kwakwa a Abuja
- Wani mutum mai suna Ajiya ya rasa ransa bayan faɗowa daga bishiyar kwakwa a yankin Kuje da ke a babban birnin tarayya Abuja
- Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe biyu na rana a lokacin da mutumin ke ƙoƙarin ɗebo kwakwa a gonarsa
- An dai samu gawar mutumin a ƙarƙashin bishiyar kwakwa da raunuka a kansa, sannan aka yi masa sutura kamar yadda addinin musulunci ya tanada
FCT - Wani mutum mai suna Ajiya ya mutu bayan faɗowa daga bishiyar kwakwa a yankin Gwargwada-Ugbada da ke Kuje a babban birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin yankin, Sa’idu Ibrahim ya ce lamarin ya faru ne ranar Asabar ɗin da ta gabata da misalin ƙarfe biyu na rana a lokacin da mutumin ke ƙoƙarin girgizo kwakwa a gonarsa, a rahoton da Daily Trust ta wallafa.
An tarar da gawar mutumin a ƙarƙashin bishiyar kwakwa
Ya ce sai bayan ƙarfe shida na yamma ne ‘yan uwan mamacin suka fahimci cewa bai dawo gida ba, daga nan ne suka sanar da ’yan banga waɗanda suka tafi zuwa gonar nan take.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ƙara da cewa, 'yan bangar sun tarar da gawarsa a ƙarƙashin bishiyar kwakwar tare da raunuka a kansa.
Shugaban ƙauyen, wato Agabe na Gwargwada-Ugbada, Alhaji Hussaini Agabi Mam, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa mamacin ɗan yayarsa ne.
Matarsa ta yi ƙoƙarin hana shi zuwa gonar
Alhaji Hussaini ya ce,
“Mamacin ɗan yayata ne. Hasali ma kamar matarsa ta san ba zai dawo ba, domin a lokacin da ya ke shirin zuwa gonar, sai da ta nemi ya haƙura da zuwa saboda cewa rana ta yi zafi sosai a lokacin.
"Amma ya dage sai ya je ɗebo kwakwar duk da cewa matarsa ta ɓoye igiyar da ya saba hawa bishiyar da ita."
Sai dai ya ce matar daga bisani ta ba shi igiyar bayan da maƙwabta suka sa baki. Tuni aka binne mamacin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Mutane biyu sun mutu sakamakon faɗowar gini a Abuja
A wani labarin da muka wallafa a baya, wani gini ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu a yankin Wuse 2 da ke Abuja.
Hukumomin agajin gaggawa da suka isa wurin da lamarin ya faru sun yi nasarar ceto wasu mutanen da ransu.
Asali: Legit.ng