Gwamnatin Tarayya Ta Kafa Sharuddan Kwaso Ragowar Yan Najeriya Daga Sudan
- Yayin da ake dab da gama aikin jigila, Gwamnatin tarayya ta gindaya sharudda uku kan duk mai son baro Sudan zuwa Najeriya
- Hakan ta faru ne bayan wasu yan Najeriya sama ko kusan 200 sun fito a baya bayan nan suna son dawowa ƙasarsu ta gado
- Tun bayan fara aikin jigilar zuwa yanzu, Gwamnatin tarayya ta dawo yan kasa sama da 2000 daga Sudan
Abuja - Gwamnatin tarayyan Najeriya, a ranar Litinin 15 ga watan Mayu, ta gindaya shaarudɗan da wajibi a cikasu gabanin kwaso ragowar mutanen da suka maƙale a Sudan.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa FG ta kafa sharuddan ne kan yan Najeriya da sai yanzu suka kawo kansu suna son dawowa gida domin tserewa yaƙin da ya ɓarke a ƙasar Sudan.
Hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje ce ta sanar da sharuɗɗan bayan adadin mutanen da suka taru sun tashi daga 26 zuwa kusan 200.
A cewar hukumar, gwamnati na dab da karƙare shirin jigiƙar wadanda yaƙi ya rutsa da su a Sudan, sai kuma aka samu karin mutane.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jerin sharuddan da FG ta kafa
1. Wajibi ka ɗauki nauyin kanka zuwa bakin ruwan Sudan
2. Wajibi ya kasance kana da karin shaidar zaman ɗan ƙasa na Najeriya
3. Dole sai kana da sahihin hanyar tuntuba ko mazauni a Najeriya.
FG ta yi namijin kokari
Kakakin hukumar kula da yan Najeriya masu zama a ƙasashen waje, AbdulRahman Balogun, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa, kamar yadda The Nation ta rahoto.
Ya bayyana irin namijin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi domin tabbatar ta kwaso kowane ɗan Najeriya daga Sudan ba tare da barin ko mutun ɗaya ba.
Ga dukkan ma su son dawowa gida daga Sudan, Balogun ya ce:
"Dole ka kai kanka bakin gabar ruwan Sudan. Dole sai kana da katin shaida na Najeriya. Dole sai kana da tabbatacciyar lamba ko mazauni a Najeriya."
A wani labarin kuma Kotu Ta Tsare Fitaccen Malamin Musulunci Na Bauchi a Kurkuku Kan Zargin Batanci Ga Annabi SAW
Rundunar yan sandan Bauchi ta gurfanar da Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi a gaban Kotu. A zaman yau, Kotu ta umarci a tsare shi a gidan gyaran hali kafin gobe Talata.
Asali: Legit.ng