Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Anambra Ya Tsallake Rijiya da Baya a Hadarin Mota
- Shugaban majalisar dokokin jihar Anambra ya tsallake rijiya da baya yayin da wata Tirela ta murkushe motar da yake ciki
- Wata majiya ta ce Honorabul Uche Okafor ya je wurin ne domin ɗauko wasu takardu na tsohon Darakta, wanda ya gamu da hatsari a wurin tun farko
- Kakakin majalisar bai ji rauni ba haka waɗanda ke tare da shi, amma motar ta lalace
Anambra - Kakakin majalisar dokokin jihar Anambra, Uche Okafor, ya tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya auku a mahaɗar titunan Agu-Awka, a Awka, Babban Birnin jihar ranar Asabar da daddare.
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa hatsarin ya yi kaca-kaca da motar kakakin majalisar ta yadda babu mai iya gane ta.
Bayanai sun tabbatar da cewa hatsarin da ya kusa rutsawa da Honorabul Okafor, shi ne na biyu da ya faru a kan mahaɗar a wannan rana ta Asabar 13 ga watan Mayu, 2023.
Wane hatsari aka yi da farko?
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tun da fari, wani tsohon Darakta a gwamnatin jihar Anambra, Chief Jude Emecheta, ne ya gamu da hatsari a wurin, wanda ta kai ga ya sume kuma motar da yake ciki ta yi raga-raga.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wata majiya ta ce bayan kakakin majalisar ya samu labarin abinda ya auku daga bakin abokin tsohon daraktan, nan take ya garzaya wurin da hatsarin ya auku tare da masu yi masa hidima.
A cewar majiyar daga zuwan tawagar kakakin, ya ɗauki Emecheta zuwa Asibiti, a hanyar dawowa daga Asibitin ne hatsarin ya sake faruwa kuma a daidai wannan wuri.
Majiyar ta ce:
"Yayin da suka kama hanyar komawa gida, shugaban majalisar ya tsaya a wurin da aka yi hatsarin domin ɗaukar wasu muhimman takardu na tsohon daraktan daga cikin motarsa kar a yi asararsu."
"Yana cikin bincikawa kawai wata Tirela ta sake kuccewa ta bigi motar da tsohon daraktan ya yi haɗari a cikinta lokacin shugaban majalisa na ciki. Haka nan babban Motar ta murkushe motar da Okafor ya zo da ita."
Kakakin majalisar ya tsira ba tare da jin ko kwarzane ba, haka zalika hadimansa amma Motar da suka je wurin a cikin ta lalace, kamar yadda rahoto ya tabbatar.
Dalilin da Yasa Muka Zabi Akpabio a Abbas a Matsayin Shugabannin Majalisa, Shettima
A wani labarin kuma Kashim Shettima Ya Bayyana Babban Abinda Ya Sa Suka Zabi Yan Takara A Majalisar Tarayya Ta 10
Har yanzu jam'iyyar APC ta gaza haɗa mambobinta a majalisar tarayya tun bayan sanar da waɗanda take goyon baya su hau kujerar shugabanci.
Zababben mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya faɗi abinda ya ja hankalin shugabannin APC har suka yanke waɗanda za'a zaɓa.
Asali: Legit.ng