Matsalar Wutar Lantarki: NERC Ta Hana DisCos Karɓar Kuɗaɗe Hannun Kwastomomin Da Aka Yankewa Wuta
- Hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa NERC, ta hana kamfanonin rarraba wuta wato DisCos, karɓar kuɗaɗe daga hannun kwastomomin da aka yankewa wuta
- Ana sa ran wannan sabuwar doka za ta kare kwastomomin da ake amsar kuɗaɗen wuta fiye da ƙima daga hannayensu
- Dokar ta kuma zo da sabbin sharuɗa ga ma'aikatan, kan yadda za su riƙa saurare da kuma kula da korafe-korafen kwastomominsu
Abuja - Hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa NERC, ta haramtawa ma'aikatan kamfanonin rarraba wutar lantarki wato DisCos, karɓar kuɗaɗe daga hannun kwastomomin da aka yankewa wuta a dalilin rashin biyan kuɗi.
Haramcin na ƙunshe ne a wata takarda da shugaban hukumar ta NERC, Sanusi Garba ya sanyawa hannu kamar yadda The Nation ta wallafa.
Sabuwar dokar za ta taimakawa masu amfani da wutar lantarki ne
"Mahmud Yakubu Tsohon Yaro Na Ne," Pater Obi Ya Fallasa Maganar da Ya Faɗa Wa Shugaban INEC Gabanin Zaben 2023
Takardar mai taken "Customer Protection Regulation 2023” ta bayyana cewa za a riƙa karɓar kuɗaɗe ne daga hannun mutum a yayin da aka mayar masa da wutarsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sannan kuma za a riƙa karɓar kuɗin bashin da ake binsa a hankali kamar yadda mai amfani da wutar ya saba biya a baya har zuwa lokacin da zai gama biyan duk abinda ake binsa.
Sannan kuma dokar ta yi tsari kan yadda za a riƙa amsar kuɗaɗen wuta daga hannun mutanen da ba sa amfani da mita wajen biyan kuɗin wutar. Ana sa ran za a rage yawan kuɗaɗen da ake karɓa daga hannun irin waɗannan mutanen.
Za a samu sauyi kan yadda ake karɓar kuɗaɗe a baya
Ana ganin hakan a matsayin wani babban sauyi a kan tsarin karɓar kuɗaɗen wutar da ake yi a baya ta yadda akan ci gaba lissafawa mutum kuɗaɗen wuta duk kuwa da cewar an yanke masa wutar.
Ana sa ran wannan sabuwar doka za ta taimaka wajen rage yawan ƙorafe-ƙorafen da jama'a ke yi kan yadda ake cajinsu kuɗaɗen wuta fiye da ƙima.
Dokar ta kuma buƙaci shuwagabanin na kamfanonin rarraba wutar lantarki su yi tsari kan yadda za su riƙa kula da basussukan da ake bin wasu kwastomomin.
Sabon tsarin yankan wuta
Vanguard ta wallafa cewa, za a bai wa kwastoma kwanaki 12 ne kafin a yanke masa wuta in bai biya kudin ba a lokacin.
Haka nan kuma, a karkashin wannan sabuwar doka, dole ne ma'aikacin wuta ya isa wuraren da aka shigar da ƙorafi kan ɗaukewar wuta a cikin sa'o'i 24 bayan sanarwar.
Idan matsalar ta faru ne a dalilin kayayyakin kamfani, to ya zama dole a maye gurbin abinda ya lalace da wani sabo a cikin sa'o'i 24.
Buhari ya kammala aikin samar da wutar lantarki
A wani labari da muka wallafa, gwamnatin shugaba Buhari ta kammala aikin samar da wuta ta Zungeru mai karfin megawats 700.
Ministan wutar lantarki na kasa injiniya Abubakar D. Aliyu ne ya sanar da haka, in da ya kuma bayyana cewa sun shirya tsaf don mika wutar ga hukumar rarraba wuta ta kasa.
Asali: Legit.ng