'Yan Sanda Sun Cafke Wani Ƙaramin Ƴaro Wanda Ya Shirya Yadda Za a Yi Garkuwa Da Shi a Jihar Delta

'Yan Sanda Sun Cafke Wani Ƙaramin Ƴaro Wanda Ya Shirya Yadda Za a Yi Garkuwa Da Shi a Jihar Delta

  • Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta samu nasarar cafke wani ƙaramin yaro wanda ya shirya yadda za a yi garkuwa da shi
  • Yaron mai suna Ade Segun ya dai haɗa baki ne da abokansa guda biyu wajen shirya wannan aika-aikar
  • Yaran da suka kitsa wannan shirin sun nemi iyayen Ade da su biya N20m a matsayin kuɗin fansa kafin su sako shi

Jihar Delta - Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta bayyana cewa ta cafke wani ƙaramin yaro, mai suna Ade Segun, mai shekara 17 tare da abokansa, Precious da Nonso bisa laifin shirya yin garkuwa da shi na ƙarya da neman N20m daga wajen iyayensa.

New Telegraph ta tattaro cewa Segun tare da abokansa suna hannun ƴan sandan bisa hannun da suke da shi a wannan aika-aikar.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

Karamin yaro ya shirya yadda za a yi garkuwa da shi a jihar Delta
Hotunan yaran da ƴan sanda suka cafke Hoto: Newtelegraph.com
Asali: UGC

Iyayen Segun sun sanar da hedikwatar ƴan sandan jihar da ke Warri halin da ake ciki bayan sun samu labarin an sace mu su ɗa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Bright Edafe, ya bayyana cewa Segun ya shirya yadda za a yi garkuwa da shi ne, tare da abokansa domin ya samu N20m daga hannun iyayensa, a ranar 9 ga watan Mayu, 2023, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa wata jami'ar ƴan sanda ce ta yi mu su shigo-shigo ba zurfi kamar za ta biya kuɗin, wanda a dalilin hakan ne aka yi ram da su.

A kalamansa:

"Wanda ake zargin, Ade Segun, ya shirya yadda za a yi garkuwa da shi tare abokansa biyu, Precious da Nonso, waɗanda suka kira iyayensa suka buƙaci su biya N20m a matsayin kuɗin fansa."
"Iyayen sun kai rahoton lamarin wajen ƴan sanda a Warri, inda wata jami'ar ƴan sanda ta nuna mu su za a biya kuɗin fansar."

Kara karanta wannan

Fitaccen Gwamnan APC Ya Naɗa Sarakunan Gargajiya Sati 2 Kafin Ya Bar Ofis

"Lokacin da jami'an ƴan sanda suka isa wajen sun yi kwanton ɓauna kan ɗaya daga cikinsu, Precious wanda ya zo ɗaukar kuɗin, inda aka cafke shi."
"Ya kai su inda Ade da ɗayan abokinsu suka ɓoye inda aka cafke su, sannan suka bayyana cewa su suka shirya komai."

Masu Garkuwa Da Mutanen Sun Bi Dare Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Da Dama a Abuja

A wani labarin na daban kuma, miyagun masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane da dama a birnin tarayya Abuja.

Masu garkuwa da mutanen sun lallaɓa ne cikin dare inda suka shiga ƙauyen Yewuti na ƙaramar hukumar Kwali, a birnin tarayya Abuja, sannan suka tafi da mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng