Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kagarko Tare Da Sace Fasto Da Wasu Mutane 21

Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kagarko Tare Da Sace Fasto Da Wasu Mutane 21

  • ‘Yan bindiga sun sake kai hari a fadar Sarkin Kagarko bayan sace ‘ya’yansa da jikokinsa a cikin kasa da mako guda
  • Maharan a wannan karo sun kai harin ne a kauyuka da dama inda suka sace Fasto da wasu mutane kimanin 21
  • Shaidan gani da ido ya tabbatar da faruwan lamarin inda ya bayyana yadda ‘yan bindigan suka sace mutanen kauyen

Jihar Kaduna - A cikin kasa da mako guda bayan ‘yan bindiga sun kai hari a fadar Sarkin Kagarko kuma suka sace ‘ya’yansa mata guda uku da jikokinsa, ‘yan bindigan sun sake kai hari a wasu kauyuka a masarautar inda suka sace Fasto da karin mutane 21.

Wani mazaunin Kagarko, Ishaka Bala ya tabbatar da haka a ranar Lahadi 14 gatan Mayu, ya ce harin ya faru ne ranar Juma’a da dare inda maharan suka mamaye kauyukan Kago da Tsauni-Abe da Doguwa da kuma Akoti.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Gano Wani Makeken Rami Da Yan ISWAP Suka Birne Makamai Masu Dimbin Yawa A Sambisa

'yan bindiga/kagarko/kaduna
Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kagarko Tare da Sace Fasto da Wasu Mutane 21 a Kaduna, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

Ya ce maharan sun kai hari wasu gidaje da dama bayan harbin kan mai uwa da wabi suka kuma sace Fasto a kauyen da wasu mutane 21, jaridar Daily Trust.

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yan bindigan ba su yi nasara ba lokacin da suka kai hari kauyen Doguwa saboda ‘yan sakai na Vigilante sun dakile harin yayin da da dama daga cikin ‘yan sakai din suka samu raunuka.”

Magatakardan sarkin ya tabbatar da kai harin 'yan bindigan a Kagarko

Makatagardan Sarkin Kagarko, Yahaya Ibrahim ya tabbatar da faruwar harin ga ‘yan jarida, sannan ya ce ya samu bayanin harin ne a ranar Asabar 13 ga watan Mayu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Muhammad Jalige bai ce komai ba game da harin bayan tuntubarsa da aka yi ta sakon karta kwana, Within Nigeria ta tattaro.

Kara karanta wannan

Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Hatsarin Mota a Jihar Bauchi

'Yan Bindiga Sun Kai Hari Fadar Kagarko Tare da Sace 'Ya'yansa da Jikokinsa

A wani labarin, 'yan bindiga sun kutsa kai cikin fadar sarkin Kagarko a kudancin jihar Kaduna yayin da suka sace 'ya'yansa da jikokinsa bayan sace wasu mutane a kauyuka.

Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindigan sun durfafi fadar sarkin Alhaji Sa'ad Abubakar suka sace 9 daga cikin 'ya'ya da jikokin sarkin sannan da wasu mutane su uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.