Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Agbeni Da Ke Jihar Oyo
- Mummunar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwar Agbeni da ke a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo
- Gobarar ta tashi ne da safiyar ranar Lahadi, inda ta bazu daga shago zuwa shago kamar wutar daji
- Jami'an kwana-kwana sun kai agajin gaggawa a kauwar, inda suka samu nasarar shawo kan gobarar
Jihar Oyo - Fitacciyar kasuwar nan ta Agbeni a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta kama da wuta.
Jaridar Punch ta tabbatar da cewa gobarar da ta tashi a kasuwar, ta fara ne da misalin ƙarfe 4:30 na safiyar ranar Lahadi.
Ko da aka tuntuɓi babban darektan hukumar ƴan kwana-kwana na jihar, Yemi Akinyemi, a wayar tarho, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Akinyemi ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa ne ta hannun wani mai gadin bankin Access dangane da gobarar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A kalamansa:
"Hukumar mu ta samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 4:37 na safiyar ranar Lahadi, ta hannun wani Sunday Ogundele, mai gadin Access Bank, cewa kasuwar Agbeni ta kama da wuta."
"Har yanzu jami'an mu na kan ƙoƙarin kashe wutar, mu na godiya sosai ga babban bankin Najeriya (CBN) reshen jihar Oyo, da suka bari mu ka yi amfani da ruwansu. Komai yana kan kular mu. Har yanzu suna zuwa CBN cigaba da samo ruwa."
Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa lamarin wanda ya auku da safiyar ranar Lahadi, ya ritsa da mutanen kasuwar da direbobin manyan motocin da suka zo sauke kaya, lokacin suna barci.
A cewar wani ganau ba jiyau ba, ya bayyana cewa wutar ta bazu da sauri kamar wutar daji, inda ta riƙa kamawa daga shago zuwa shago.
Ba a san iyakar dukiyar da aka yi asara ba a dalilin gobarar, amma shaidu sun tabbatar da cewa an yi asarar miliyoyin naira.
Fitacciyar Kasuwar Kasa da Kasa a Najeriya Ta Kama da Wuta
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa fitacciyar kasuwar nan ta 'Alaba International Market' ta kama da wuta.
Ƴan kasuwar da ke hada-hadar kasuwancin su a kasuwar sun yi ƙoƙarin daƙile ta kafin isowar jami'an kwana-kwana.
Asali: Legit.ng