Gwamnatin Buhari Ta Kammala Aikin Samar da Wutar Lantarki 1 da Ta Yi Alkawari Kafin Karewar Mulki
- An kammala aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 700 na Zungeru da ke jihar Neja a Arewacin Najeriya
- Ministan wutar lantarki Engr. Abubakar D. Aliyu ne ya sanar da hakan a wata ziyarar aiki da ya kai cibiyar
- Ministan ya samu rakiyar gwamnan jihar ta Neja Abubakar Bello da kuma Sanata Gabriel Suswam wanda shine shugaban kwamitin kula da harkokin wuta a majalisar dattawa
Neja, Zungeru - Ministan wutar lantarki Injiniya. Abubakar D. Aliyu ya sanar da cewa, an kammala aikin samar da wutar lantarki mai karfin megawatts 700 na Zungeru.
A cewar ministan, tuni kamfanin rarraba wutar lantarkin na Najeriya (TCN) a shirye yake ya karbi wutar da aka samar daga cibiyar samar da wutar lantarkin.
Ya kuma ce hakan zai cike gibin da ake samu na bukatun wutar lantarkin kasar, kamar yadda Legit.ng ta samo.
Atiku Bai Cire Rai Ba, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Ya Faɗi Abu 1 Rak da Zai Baiwa PDP Nasara a Kotu
Injiniya ya fadi haka ne a ranar Asabar, 13 ga watan Mayu a jihar Neja a lokacin da yake bayani bayan ziyarar duba aikin da aka kammala.
A lokacin ziyarar, yana tare da gwamnan jihar Abubakar Sani da kuma wasu manyan jiga-jigan majalisar da ke kula da ayyukan makamashi a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kammala komai, saura kaddamarwa
Da yake karin haske, ya ce an kammala dukkan gwaje-gwaje na aiki da na’urorin da ake amfani dasu, kuma za a kaddamar da aikin nan ba da jimawa ba a hukumance.
A cewarsa, tun shekarun 1960 rabon da Najeriya ta yi irin wannan aikin, amma sai gashi ya samu a karkashin jagorancin Buhari
Hakazalika, ya ce, gwamnatin Najeriya ta zuba dimbin hannun jari a wannan aikin na Zungeru don ta inganta samun wutar lantarki a kasar.
A gefe guda, ya ce irin wadannan ayyuka na daga buri da kudurin Buhari na ciyar da Najeriya gaba a karkashin ikonsa.
Meye amfanin wannan aikin?
Baya ga samar da karin wutar lantarki ga ‘yan Najeriya, aikin a halin yanzu ya samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya da dama kuma zai samar da hanyoyin magance ambaliyar ruwa, ban ruwa a noman rani, da kuma samar da ruwa wadatacce.
A nasa bangaren, gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya yabawa shugaba Buhari kan kammala aikin samar da wutar lantarkin mai karfin megawatt 700 na Zungeru ta jihar Neja.
A tun farko, gwamnatin Najeriya ta bayyana yadda aikin wutar lantarkin ke cin kudi da kuma yadda 'yan Najeriya ke shakku.
Asali: Legit.ng