Fitaccen Gwamnan APC Ya Naɗa Sarakunan Gargajiya Sati 2 Kafin Ya Bar Ofis
- Gwamna Simong Lalong ya ce naɗe-naɗen da ya yi na daga cikin abubuwan da wasu yankunan suka daɗe suna buƙatar a yi musu
- Lalong ya ce dama gwamantinsa ta yi alƙawari tun a can baya cewa za ta bayar da muƙaman na sarautar gargajiya a wasu yankunan jihar
- Ya ce babu yankunan da ba a ba wa sarautar ba daga cikin waɗanda aka ma alƙawari sai dai in da suke fama da rigingimu a tsakaninsu
Filato, Jos - Gwamnan jihar Filato mai barin gado, Simong Lalong, ya naɗa sarakunan gargajiya a wasu sassa na jihar, sati biyu gabanin barinsa ofis.
An bayar da sandar ƙarin girma ga sarakuna guda biyu na ƙaramar hukumar Jos ta kudu, Dagwom Rwey na Gyel, Da Nga Dangyang zuwa mai daraja ta 2. Sannan an ƙara wa Gwom Rwey na Zawan, Da Christopher Mancha, zuwa mai daraja ta 3 Daily Trust ta yi rahoto.
Alƙawuran da muka ɗauka ne muke cikawa
Da ya ke magana a yayin taron, gwamnan ya ce waɗannan naɗe-naɗe na daga cikin alƙawuran da ya yi na cika gurin da wasu masarautun ke ta fatan a cika musu na ganin an ɗaga darajarsu kamar yadda dokar ƙasa ta tanada.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma ce a matsayin ɗaya daga cikin ayyukansa na ƙarshe da ya gabatar, ya yi matuƙar farin ciki cewa mutanen Gyel da na Zawan sun shaida cewa alƙawarin da ya yi musu a baya na cewa zai ƙirƙiri masarautu ba alƙawari ba ne na siyasa.
Ya ce ba alƙawari ba ne na siyasa face alƙawarin da ya ɗauka saboda sha'awarsa ta ganin cewa shugabancinsa ya isa kowane mataki sannan domin tabbatar da cewa kowa da kowa an tafi da shi.
Yace Kamar dai yadda ya sha faɗa, masarautun gargajiya na da matuƙar muhimmanci musamman ma wajen kiyaye al'adu da kuma mutuncin al'umma.
Ina da burin dawo da darajar masarautu da al'adu
Gwamnan ya kuma bayyana cewa tun lokacin da ya hau kan karagar mulki, ya fi mayar da hankali ɓangaren dawo da darajar masarautun gargajiya domin samun cigaba a harkokin gwamnatinsa.
Lalong ya kuma ce sun ƙirƙiri masarautun dagattai guda 285, sannan sun dawo da masarautu 2 masu daraja ta ɗaya, masu daraja ta biyu guda 6, da kuma masu daraja ta 3 guda 10 a faɗin jihar.
Sannan ya ce duk da ƙoƙarin da gwamnatinsa ta yi na ganin ta naɗa shuwagabanni a duka masarautun jihar, hakan bai samu ba sakamakon rigingimu da kuma shari'o'in da ba a ƙarƙare ba a wasu masarautun.
Daga ƙarshe Lalong ya ce za su cigaba da ƙoƙarin ganin an samu daidaito a masarautun da ake fama da rigingimu domin amfanin yankunansu.
An samu asarar rayuka kan rikicin sarauta
A wani labari da muka wallafa a baya, kunji yadda rikicin sarauta ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane da kuma raunata wasu a jihar Bauchi.
Haka nan kuma jami'an tsaro sun ce an ƙona gidaje aƙalla 64 a sanadiyyar rikicin.
Asali: Legit.ng