Gidajen Gyaran Hali: Daga Yanzu Jihohi Ne Za Su Riƙa Ciyar Da Fursunoni, Ministan Cikin Gida, Aregbesola

Gidajen Gyaran Hali: Daga Yanzu Jihohi Ne Za Su Riƙa Ciyar Da Fursunoni, Ministan Cikin Gida, Aregbesola

  • Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, ya ce daga yanzu gwamnatocin jihohi ne za su riƙa kula da abinci da kuma makwancin fursunoninsu
  • Ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na kwana biyu kan batun rage cunkuso a gidajen gyaran hali da ya gudana a Abuja
  • Ministan ya kuma ce duk jihar da ba ta da gidan gyaran hali, za ta riƙa biyan gwamnatin tarayya domin kula da fursunoninta

FCT, Abuja - Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya bayyana cewa daga yanzu gwamnatocin jihohi ne za su riƙa ciyar da fursunonin jihohinsu da kuma kula da wurin zamansu.

Ya ce hakan ya biyo bayan wani zama da aka yi don gudanar da wasu gyare-gyare da aka yi wa tsarin gudanarwar gidajen gyaran halin.

Rauf Aregbesola/Gidan gyaran hali/Najeriya/Gwamnatin Tarayyar Najeriya
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya ce jihohi ne za su fara ciyar da fursunoni. Hoto: Vanguard
Source: UGC

Aregbesola ya dai yi wannan bayani ne a wajen wani taro na kwana biyu na masu ruwa da tsaki a gudanarwar gidajen gyaran hali a Abuja, kan batun rage cunkuson da ake samu a gidajen, kamar yadda ya ke ƙunshe a rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

An Yi Mamaki Yayin Da Gwamnatin Buhari Ta Ware N22.4bn Don Ciyar Da Fursunoni

Kowace jiha za ta kula da fursunoninta

Ya ce daga yanzu, kowace jiha za ta riƙa ɗaukar nauyin kula da duk wasu abubuwa na gidajen gyaran halin da ke jihohinsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda This Day ta wallafa, ministan ya ce jihohin da ba su da gidajen gyaran hali, za su riƙa biyan gwamnatin tarayya kudin abinci da kuma makwancin fursunoninsu.

Aregbesola ya ƙara da cewa wannan tsarin da aka yi zai taimaka sosai wajen ragewa gwamnatin tarayya nauyin ciyar da fursunonin da ta ke yi da kuma ba su makwanci.

Kamfanin dillancin labara na ƙasa NAN, ya wallafa wani labari da ke cewa gwamnatin tarayya ta ware N22.4bn don ciyar da fursunoni da ke tsare a gidaje 224 da ake da su a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ministan ya kuma koka kan yadda gidajen gyaran halin ke wawusar maƙudan kuɗaɗe daga lalitar gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Ake Bada Kwangilolin Biliyoyi a Karshen Mulkinmu – Gwamnatin Buhari

Har ya zuwa yanzu gwamnatin tarayya ce ke kula da gidajen gyaran halin

Aregbesola ya kuma bayyana cewa:

“Gwamnatin tarayya ce ke kula da duka gidajen gyaran halin. Ya na da kyau mutane su sani cewa akwai laifuka na gwamnatin tarayya sannan kuma akwai na jihohi kamar yadda tsarin doka ya tanada.”
“Amma har zuwa lokacin da aka kawo wannan sabon tsari, gwamnatin tarayya ce ke kula da duka gidajen gyaran halin.”

Aregbesola ya ce a cikin wannan sabuwar doka ta gidajen gyaran hali, gwamnatin tarayya ta ware wasu kuɗaɗe ga jihohi domin gina gidajen gyaran halin da za su riƙa ajiye masu laifin da ya shafi jihohinsu.

Ya kuma ƙara da cewa sashi na 12 (4-12) na dokokin gudanar da gidajen gyaran hali, ya bai wa hukumar ikon ƙin karɓar fursunoni a yayin da gidajen gyaran halin suka cika.

Gwamnati za ta kashe N22.4bn wajen ciyar da fursunoni

A labarin da muka wallafa jiya Alhamis, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta ware zunzurutun kuɗi har N22.4bn don ciyar da fursunonin gidajen gyaran hali da ke a sassa daban-daban na ƙasar nan.

ya bayyana hakan a yayin wani taro kan batun rage cunkuso a gidajen gyaran hali 224 da ake da su a Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng