Kiyaye Haɗura: A Sanya Dokokin Shari'a Wajen Hukunta Masu Karya Ƙa'idojin Hanya, Kwamandan FRSC
- Shugaban hukumar kiyaye haɗura shiyyar Bauchi Yusuf Abdullahi, ya ce amfani da dokokin shari'ar Muslunci zai taimaka wajen rage afkuwar haɗura
- Ya ce dokokin na shari'a za su sanya direbobi da ke tuƙin ganganci su natsu sannan kuma su shiga taitayinsu
- Abdullahi ya kuma ce hukuncin zai sanya duk wanda aka samu da laifi a faruwar haɗari janyo ma 'yan uwansa biyan diyya koda ace shi ya mutu
Bauchi - Shugaban shiyyar Bauchi na hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa, Mista Yusuf Abdullahi, ya yi kira da a sanya dokokin shari'ar Muslunci wajen hukunta masu karya dokokin tuƙi.
Abdullahi ya dai yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ranar Alhamis a Bauchi jaridar Punch ta wallafa.
Dokokin da aka tanada sunyi sauƙi da yawa
Ya ce dokokin da aka tanadar don hukunta masu karya ƙa'idojin tuƙi sunyi sauƙi da yawa, a saboda haka ne ya ke ganin buƙatar a shigo da dokokin shari'a a ciki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya bayyana cewa hakan zai taimaka wajen sanya direbobi su riƙa mutunta ƙa'idojin tuƙi da kuma yin tuƙin kamar yadda ya kamata.
Ya kuma ce dokokin za su sa a rage samun yawaitar munanan haɗura da ake samu a titunanmu sakamakon tuƙin ganganci.
A cewarsa:
“Idan aka kawo dokokin shari'a cikin dokokin tuƙi, mutane za su farka daga baccin da suke yi. Mutanenmu na ganganci sosai, kuma masu motocin ba su cika bincikar direbobin ba.”
“Idan ba dokokin shari'a aka sanya cikin dokin tuƙi ba, da yawa daga cikin direbobi za su ci gaba da tuƙi yadda suka ga dama.”
Ban Yi Nadama Ba: Mutumin Da Ya Taka Daga Gombe Zuwa Abuja Domin Buhari Ya Ce Zai Maimaita Idan Ya Samu Dama
Idan direba yayi laifi, hukunci zai shafi har uwansa
Abdullahi ya ƙara da cewa kawo dokokin shari'ar cikin dokokin tuƙi zai yi maganin munanan ɗaɓi'un da akan samu wasu direbobi da kuma sauran masu amfani da tituna da su, waɗanda su ne ke jayo haɗurra a lokuta da dama.
Ya ce a hukuncin shari'a duk wanda aka samu da laifi a faruwar haɗari, ba shi kaɗai ba har 'yan uwansa sai laifin da ya aikata ya shafesu wajen biyan diyya da makamantan hakan.
Idan kuma ya zamto direban da ya sabbaba haɗarin ya mutu, to mai motar ne zai biya diyya tunda alamu sun nuna bai bashi horon da ya dace ba.
Daga ƙarshe, ya bayyana cewa idan aka yi duba ya zuwa ƙasashen da suke amfani da dokokin na shari'a za a ga yadda kowa ke yin taka tsan-tsan, saboda sun san cewa babu wani rangwame da mai laifin zai iya samu kamar yadda Guardian ta yi rahoto.
Haɗuran mota sun jawo rasa rayukan mutane da dama
A wani labari da muka wallafa a ƙarshen watan Maris, hukumar kiyaye aukuwar haɗura ta jihar Bauchi ta sanar da faruwar haɗuran mota da suka yi sanadiyar rasa rayukan jama'a da dama.
Haɗuran dai sun faru ne a sassa daban-daban na jihar ta Bauchi.
Asali: Legit.ng