Rikicin Sudan: Da Alamu Za A Ƙara Wa Mahajjatan Bana Na Najeriya Kuɗin Jirgi

Rikicin Sudan: Da Alamu Za A Ƙara Wa Mahajjatan Bana Na Najeriya Kuɗin Jirgi

  • Kwamishinan tsare-tsare a hukumar Alhazan Najeriya, Abdullahi Magaji Harɗawa ya ce akwai yiwuwar kowane mahajjaci ya samu ƙarin kuɗi akan wadanda ya biya a baya
  • Haraji da za a biya ƙasashe da kuma ƙarin nisa da ze janyo ƙarin shan man jirgi ne za su sa a ƙara kuɗin jigilar mahajjatan
  • Har yanzu ba a gama yanke shawarar cewa ko a gurin wa za a karɓi waɗannan ƙarin kuɗaɗen ba

FCT, Abuja - Hukumar aikin hajji ta ƙasa ta ce akwai yiwuwar rikicin da ake yi a Sudan ya shafi masu zuwa aikin hajji a bana wajen yiwuwar samun ƙarin kuɗin jirgi zuwa ƙasa mai tsarki.

A zaman da aka gudanar yau, tsakanin hukumar Alhazai ta ƙasa da kuma da hukumar da ke kula da kamfanonin jiragen sama ta ƙasa, an samu amincewa kan jigilar maniyyatan na bana.

Kara karanta wannan

Zaɓen Shugaban Kasa: Atiku Ya Ɗauki Manyan Lauyoyi 19 Don Kwace Nasara Daga Hannun Tinubu A Kotu, Jerin Sunaye

Hajj Commission
Aikin Hajji. Hoto: National Hajj Commission
Asali: Facebook

Zagaye da za a yi ya jawo ƙarin kuɗin

Sai dai hukumar alhazan ta ce akwai yiwuwar a ƙara karɓar karin wasu kuɗaɗen daga hannun maniyyatan sakamakon zagaye da za'a yi da kuma wasu ƙarin kuɗaɗe da za a kashe a yayin jigilar mahajjatan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kwamishinan hukumar kula da tsare-tsare na hukumar Alhazan Abdullahi Magaji Hardawa, ya shaidawa BBC Hausa cewa akwai yiwuwar a yi zagaye muddun har aka kai lokacin da za a fara jigilar mahajjatan na bana ba tare da an samu izinin bi ta sararin samaniyar ƙasa Sudan ba.

Ya ƙara da cewa ƙasar ta Sudan ta rufe sararin samaniyar ta yadda babu wani jirgi da ze iya bi ta can saboda gudun matsala sakamakon rikicin da ke faruwa a can.

Za a biya harajin sararin samaniya

Kara karanta wannan

Majalisa ta 10: Kakaba Shugabannin Majalisar Wakilai Ya Kawo Rudani a APC, Wasu 'Yan Takara Sun Yi Bore

Harɗawa ya ce duk ƙasar da za a bi ta sararin samaniyar ta to dole ne a biya ta wani haraji, wanda kuma idan ba a bi ta Sudan ba, yawan ƙasashen da za a ratsa ta cikinsu zai ƙaru.

Haka nan ya kuma ce idan ba a bi ta Sudan ba, nisan tafiyar ya ƙaru, wanda dole za a samu ƙarin shan mai da ze isa akai mahajjatan zuwa ƙasa mai tsarki. A bisa waɗannan dalilai ne kamfanonin jiragen suka buƙaci dole a ƙara musu kuɗi.

Ya bayyana cewa har yanzu ba a gama yanke shawara kan cewa ko a wajen mahajjatan za a karɓi waɗannan ƙarin kuɗaɗen ba ko a'a.

A ranar 21 ga watan Mayu da muke ciki ne dai ake sa ran fara jigilar mahajjatan daga filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, kamar yadda hukumar Alhazan ta sanar a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Faragaba Ta Ƙaru, Hukumar Sojin Najeriya Ta Fallasa Masu Hannu a Shirin Hana Rantsar da Bola Tinubu

Kamfanonin jiragen sama sun ki sanya hannu da farko

Da farko dai kamfanonin jiragen saman da aka amince su yi jigilar mahajjatan na bana sun ki yarda su sanya hannu.

Kamfanonin da za su yi jigilar a bana sune Azman Air, Air Peace, Max Air da kuma Aero Contractors.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng