Da Dumi-Dumi: Mutane 40 Sun Nutse a Wani Hadarin Jirgin Ruwa a Jihar Sokoto

Da Dumi-Dumi: Mutane 40 Sun Nutse a Wani Hadarin Jirgin Ruwa a Jihar Sokoto

  • Ƴan mata 40 sun nutse cikin ruwa a wani mummunan haɗarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Sokoto
  • Lamarin ya auku ne lokacin da kwale-kwalen da ke ɗauke da ƴan matan waɗanda suka fito samo itace ya kife
  • An samu an tsamo gawarwakin mutum 15 daga cikin waɗanda lamarin ya ritsa da su, yayin da ake ta ƙoƙarin ciro sauran

Jihar Sokoto - Ƴan mata 40 sun nutse cikin ruwa a wani haɗarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Sokoto.

Jaridar Aminiya ta kawo rahoto cewa, mutanen cikin jirgin da suka nutse sun tashi ne daga ƙauyen Dundeji inda za su je Kambama, a ƙaramar hukumar Shagari cikin jihar Sokoto.

Mutum 20 sun nutse a wani hadarin jirgin ruwa a Sokoto
Jirgin ya nutse ne dauke da mutum 40 Hoto: Premium times
Asali: UGC

Ƴan matam sun fita daga cikin gidajensu domin samo itacen girki a ranar Talata da misalin 12 na rana, sai kawai jirgin ya kife da su a cikin ruwan inda suka nutse gaba ɗaya.

Kara karanta wannan

Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Haɗarin Kwale-kwale a Zamfara

Masu gudanar da aikin ceto sun samu nasarar ciro gawarwakin mutum 15 daga cikin mutanen da suka nutse a cikin ruwan, inda yanzu haka ake neman ragowar mutum biyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Punch ta ce mutanen da ke cikin kwale-kwalen ƴan mata waɗanda suka fita neman iccen girki. 15 daga cikin su sun riga mu gidan gaskiya, yayin da ake cigaba da neman ciro ragowar ƴan matan da suka nutse a cikin ruwan.

Majiyoyi masu ƙarfi sun tabbatar da cewa, akwai sama da ƴan mata 40 a cikin kwale-kwalen lokacin da haɗarin ya auku.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa waɗanda suka ƙware a harkar ninkaya cikin ruwa, sun tsamo gawarwakin ƴan mata 15 daga cikin waɗanda suma nutse a cikin ruwan, yayin da ake cigaba da ƙoƙarin lalubo sauran.

Shugaban ƙaramar hukumar Shagari, Aliyu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar haɗarin, inda ya ce an soma shirye-shiryen gudanar da jana’izar mamatan waɗanda suka gamu da ajalin su a haɗarin jirgin.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka Da Gudanar Da Ibada, 'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Masu Gudanar Da Bauta a Arewacin Najeriya

Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Haɗarin Kwale-kwale a Zamfara

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa mutum 8 sun kwanta dama a wani haɗarin jirgin kwale-kwale a jihar Zamfara.

Lamarin dai ya auku ne a cikin birnin Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng