English, 98; Biology, 94: Daliba ’Yar Shekara 16 Ce Ta Fi Kowa Cin Jarrabawar JAMB
- Ejikeme Joy, wata daliba a makarantar sakandare ta mata ta Anglican a karamar hukumar Nnewi a jihar Anambra ta fi kowa cin jarrabawar UTME a bana
- Joy ta samu maki mai daukar hankali a dukkan darussa hudu da ta rubuta, inda ya samu jumillar maki 362 a UTME
- Kwamishinan ilimi a jihar Anambra, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, ta yi martani game da kwazon wannan daliba
Nnewi, jihar Anambra – Wata daliba a makarantar sakandaren mata ta Anglican da ke Nnewi a jihar Anambra, Ejimeke Joy ya dauki hankalin jama’a bayan lashe maki mai tsoka jarrabawar UTME.
Rahoton da Legit.ng Hausa ke samu ya bayyana cewa, dalibar ta samu maki 362 a jarrabawar da hukumar JAMB ke shirya a duk shekara.
Wakilinmu a jihar Anambra, Mokwugwo Solomon ya gano adadin makin da dalibai ta samu kan kowane darasi da ta rubuta a jarrabawar.
Makin da Joy ta samu
- English - 98
- Physics - 89
- Biology - 94
- Chemistry – 81
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gwamnatin Anambra ta yi martani
Wata sanarwar da sakataren yada labarai ga gwamna Charles Soludo. Christian Aburime a ranar Asabar ta yaba da kokarin da dalibai ta yi wajen nuna kwazo a jarrabawar.
Hakazalika, sanarwatr ta bayyana alfahari da dalibai da kuma bayyana irin tasirin da gwamna Soludo ke yi wajen ciyar da ilimi gaba a jihar da ke Kudancin Najeriya.
Idan baku manta ba, hukuamar jarrabawa ta JAMB ta saki sakamakon jarrabawar daliban da suka rubuta UTME na shiga makarantun gaba da sakandare a bana.
Hakan ya dauki hankali matuka, inda daliban da yawa ke bayyana adadin makin da suka samu a wannan shekarar.
Yadda ake duba sakamakon UTME na 2023
Ekweremadu: Abu 5 Game Da Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawar Najeriya Da Aka Yanke Wa Shekara 10 a Birtaniya
A wani labarin, mun kawo muku yadda ake duba sakamakon jarrabawar UTME ta 2023 da aka rubuta a wannan shekarar cikin watan Afrilun da ya gabata.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar da hukumar ta fitar, inda ta bayyana yadda ake duba sakamakon da kuma wadanda ba za su samu damar ganin sakamakon jarrabawar ba saboda wasu dalilai.
A cewar JAMB, duk dalibin da ke son duba sakamakonsa, to zai tura sakon tes ne da layin da ya yi rajistar UTME a bana (UTMERESULT zuwa lamba 55019 ko 66019).
Asali: Legit.ng