Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Ragargaji Gwamnatin Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

Kungiyar Ibo Ta Najeriya Ta Ragargaji Gwamnatin Buhari Kan Hukuncin Ekweremadu, Ta Bayyana Mataki Na Gaba

  • Kungiyar kabilar Ibo ta caccaki gwamnatin tarayya na rashin yin katabus don taimakon Ekweremadu, wanda ya yi aiki tukuru a kasar nan don kawo cigaba
  • Kungiyar ta bayyan hukuncin da aka yanke masa na tsawon shekaru 10 a gidan kaso abun takaici da kuma bakin ciki
  • Ta kara da cewa kungiyar za ta kai masa ziyara nan kusa, da karfin guiwan cewa Ekweremadu zai ci wannan jarabawa da ya same shi.

Jihar Enugu – Kungiyar hadin kai da cigaban al’adun kabilar Ibo a Najeriya, Ohanaze Ndigbo, a ranar Asabar 6 ga watan Mayu ta caccaki Gwamnatin Tarayya na yin burus wurin taimakon tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu.

Jaridar Legit ta ruwaito yadda kotu a Burtaniya ranar Juma’a ta yanke wa Ekweremadu daurin shekaru 9 a gidan kaso tare da matarsa Beatrice, wadda aka yanke mata na tsawon shekaru 4 da watanni 6 bayan da ta dau nauyin wani matashi daga Najeriya don cire masa koda don ceto ‘yarsu da ke fama da rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Wawure Kudaden Fansho: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Daurin Da Aka Yi Wa Maina Na Shekaru 8

buhari/ike
Buhari da Ekweremadu, Hoto: Facebook
Asali: Facebook

Sannan likitan da ke kula dasu shima an yanke masa hukuncin daurin shekaru goma a gidan kaso.

Da take maida martani, kungiyar Ohanaze Ndigbo ta bakin kakakinta, Alex Obinna, ta ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen ceto dan kabilar nasu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Obinna, a lokacin da yake zantawa da jaridar Punch ya ce:

"Gwamnatin Tarayya ba su dauke Ekweremadu da mutunci ba a matsyinsa na tsohon mataimakin shugaban majalisa da ya yi aiki tukuru, maimakon haka su ma sai suka fito da nasu korafin cin hanci akan Ekweremadu tare da kwace kadarorinsa.”
“Wannan mutumin ya na tare da ku na tsawon lokaci, a dai dai lokacin da yake bukatar taimakonku sai kuka bijiro da wasu abubuwa har da kwace masa kadarorinsa”
“Duk wadannan abubauwa da ke faruwa ya nuna cewa ba iya Burtaniya ce kadai ke nemansa ba, har da gwamnatin tarayyar Najeriya”

Kara karanta wannan

Diyar Ekweremadu Sonia Ta Magantu Yayin da Kotun Birtaniya Ta Aika Iyayenta Magarkama, Bidiyo Ya Bayyana

Hukuncin kotun Burtaniya bai yi dadi ba

Kungiyar ta bayyana wannan hukunci da ‘abun takaici kuma mai radadi’ kakakin ya kara da cewa shugabanninsu za su kai wa Ekweremadu ziyara nan ba da dadewa ba, kuma a karshe zai fita a cikin wannan yanayi cikin karfi da kuma lafiya.

Ya kara da cewa:

“Kafun yanzu, duk da ba a kungiyance ba mun sha kai masa ziyara a gidan yari, kuma zamu sake komawa ko da bayan ya fara wa’adinsa na gidan kaso.”
“Abun takaici ne kuma mai radadi a ce dan kabilar Ibo mai wannan matsayi an yanke masa irin wannan hukunci, duk da ba abun da zamu iya yi a yanzu.”

Abubuwa 5 Mafi Muhimmanci Da Baku Sani Ba Game Da Sanata Ike Ekeweremadu Da Matarsa

A wani rahoto kuma, A ranar Alhamis 23 ga watan Yuni na 2022 ne kafar sada zumunta ta zamani ta dau zafi bayan da aka samu labarin kama tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice.

Bayan dukkan wadannan abubuwa da suka dabaibaye sanatan, akwai tarun abubuwan masu ban sha’awa tattare da ma’auratan, ciki har da siyasa da iyalinsa da ilimi da kuma sauran lambobin yabo da ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.