Gwamnan Kwara Ya Nadawa Shahararren Dan Kasuwar Kaduna Sarauta
- Alhaji Buhari Adeniyi ya zama sabon Onijagbo na Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar Kwara
- Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya amince shahararren dan kasuwar mazaunin Kaduna ya maye gurbin tsohon Onijagbo na Ijagbo, Oba Salaudeen Fagbemi Adeyeye
- Manyan mutane hudu ne suka yi takarar kujerar daga gidan sarautar Ifeyode na Bara
Kwara - Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da nadin Alhaji Buhari Adeniyi a matsayin sabon Onijagbo na Ijagbo da ke karamar hukumar Oyun ta jihar.
Sabon basaraken wanda ya kasance dan kasuwa mazaunin Kaduna, ya yi nasara ne bayan ya gwabza da sauran yan takara.
Shine zai maye gurbin tsohon Onijagbo na Ijagbo, Oba Salaudeen Fagbemi Adeyeye, wanda ya mutu a watan Disamba, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarauta da ci gaban al'umma, Hon. Lafia Aliyu Kora-Sabi, ne ya sanar da nadin Adeniyi a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 5 ga watan Mayu. Ya ce sanarwar ta bi tsare-tsare masu tsawo da doka ta tanadar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamna Abdulrazaq ya taya sabon Onijagbo murna
A cewar sanarwar, gwamnan ya taya sabon sarkin murna kan nadin da aka yi masa sannan ya bukace shi da ya gina gadar aminci a ciki da wajen daularsa.
Sanarwar ta ce:
"Wannan babban matsayin ya sanya mai martaba sarki a gurbin da zai gina gadoji na jituwa, fahimta, juriya, da zaman lafiya a tsakanin mutanen.
"Gwamnan ya kuma bukaci 'ya'yan garin mai dadadden tarihi da su yi aiki tare da mai martaba sarki don dorawa kan nasarorin iyaye da kakanninsu."
Gwamnan ya roki Allah ya sa mulkin sabon Onijagbo ya kawo ci gaba, zaman lafiya da nasara ga mutanensa na Oyun da ma jiharsa baki daya, rahoton Tribune.
Jerin mutanen da suka yi takarar kujerar Onijagbo
Yan takara hudu ne aka zaba domin zama kan kujerar Onijagbo wanda sarki ya yanke shawara.
Sauran abokan karawarsa sune Sarafadeen Adebayo Sanni, wani lauya mazaunin Ibadan, Shehu AbdulSalam mazaunin New York da Alhaji Rafiu Jimoh Daunsi, ma'aikacin gwamnati mai ritaya daga ma'aikatar ruwa, Ilorin, dukkansu sun fito daga gidan sarautar Ifeyode na Bara.
A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sabonta wa'adin mambobin majalisar asusun lamunin yan sanda na wasu shekaru uku masu zuwa.
Asali: Legit.ng