Lauyoyi 50 Za Su Kare Nasarar Cin Zaben Shugaban Kasa Na Tinubu: Sunayen Manya 17 Daga Cikinsu Ya Fito
- Babban lauya, Wole Olanipekun zai jagoranci wasu daga cikin abokan shi lauyoyi zuwa kare nasarar zaɓen Tinubu
- Idan ba a manta ba, INEC ta sanar da Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe
- Sai dai kuma Peter Obi na Labour Party da Atiku Abubakar na PDP sun yi watsi da sakamakon zaɓen
Biyo bayan watsi da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da 'yan adawa su ka yi, Wole Olanipekun tare da wasu lauyoyi su 49 sun shirya tsaf domin kare nasarar da Tinubu ya samu a kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.
Sai dai 'yan takarar PDP Atiku Abubakar da kuma na Labour party Peter Obi ba su gamsu sakamakon da aka bayyana ba na cewar Bola Tinubu na jam'iyyar APC ne ya lashe zaɓen da ya gudana a 25 ga watan Fabrairun 2023.
Shiri Ya Kwabe: Jigon Jam'iyya Ya Garzaya Kotu Neman a Dawo Masa Da Kayayyakin Da Ya Raba Lokacin Zabe
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tinubu ya doke Atiku da Obi da ƙuri'u da dama
Kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa, Tinubu ya samu ƙuri'u 8,794,726 wanda hakan ne ya ba shi damar doke abokan hamayyar shi Atiku Abubakar da ya zo na biyu da ƙuri'u 6,984,520 da kuma Peter Obi da ya zo na uku da ƙuri'u 6,101,533.
A sabili da haka an samu wasu lauyoyi da su ka bayyana ra'ayin su na son tsaya ma zaɓaɓɓen shugaban don kare ma shi nasarar ta shi a gaban kotu, waɗanda kuma yanzu haka su na jiran Atiku da Obi su shigar da ƙara ne kawai. Legit ta samu damar tattaro mu ku sunayen waɗannan lauyoyi.
Lauyoyin da suke son kare Tinubu
Ga wasu 17 daga cikin jerin manyan lauyoyin da su ke son kare Tinubun kamar haka:
- Wole Olanipekun
- Akin Olujimi
- Yusuf Ali,
- Lateef Fagbemi
- A.U. Mustapha
- Ahmed Raji
- Abiodun Owonikoko
- Kemi Pinheiro
- Niyi Akintola
- H.M. Liman
- Taiwo Osipitan
- Babatunde Ogala
- Roland Otaru
- James Onoja
- Muiz Banire
- Olusola Oke
- Mohammed Abubakar.
Shirye mu ke mu yi maganin duk wani mai son kawo hargitsi
Awani labarin kuma, Sojoji sun gargaɗi duk masu yinƙurin kawo hatsaniyar da ka iya kawo cikas a bikin rantsar da sabuwar gwamnati da ke zuwa a 29 ga watan Mayun nan da mu ke ciki.
Hukumar ta ce jami'an ta na nan cikin shirin ko ta kwana domin tunkurar kowace irin matsala da ma su son kawo ruɗanin suke tunanin sun tanada.
Asali: Legit.ng